Hon Kalu ya zama mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Majalisar Wakilai ta Ƙasa sun zaɓi Hon Benjamin Kalu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai.

Kalu ɗan Jam’iyyar APC ne mai wakiltar Mazaɓar Bende daga Jihar Abia.

Kuma ya samu zama Mataimakin Majalisar ne ba tare da hamayya ba.

Tuni Akawun Majalisar, Sani Tambuwal, ya rantsar da Kalu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai don kama aiki.

Kalu ya gaji Idris Wase ne wanda ya riƙe matsayin a Majalisa ta tara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *