Bana babu hawan Babbar Sallah a Masarautar Zazzau

*Sarkin zazzau zai tafi ƙasa mai tsarki

Masarautar Zazzau, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, LLD, ta ba da sanarwar cewar, ba za a gudanar da hawa ba yayin Babbar Sallah mai zuwa.

Hakan zai faru ne sakamakon tafiya aikin Hajjin da Sarkin Zazzau zai yi don sauke farali, in ji sanarwar da masarautar ta fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, “Ba za a yi hawan Sallah Babba ba, kamar yadda Maimartaba Sarkin Zazzau ya saba jagorantan Hawan a duk shekara.

“Maimartaba Sarkin Zazzau na yi wa kowa fatan Alhairi, da fatan za a ci gaba da yin addu’o’i domin samun cikakken zaman lafiya a ƙasarmu baki ɗaya.

“Da fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya, amin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *