Tajuddeen Abbas ya zama shugaban Majalisar Wakilai

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Wakilai ta zaɓi Tajuddeen Abbas, na Jam’iyyar APC a matsayin Shugaban Majalisar.

Abbas ya taki wannan matsayi ne bayan da ya doke abokan hamayyarsa, Aminu Jaji da Ahmed Idris Wase.

Yayin da Abbas ya samu ƙuri’u 353, Aminu Jaji ya samu uku, haka ma Jibrin Wase.

Baki ɗaya, ƙuri’i 359 aka kaɗa a zaɓen.

Abbas shi ne ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Zariya a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *