An rantsar da Sanata Barau a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Daga BASHIR ISAH

Zaɓaɓɓen sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Jibrin Barau, ya lashe zaɓen mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Sanata Dave Umahi ne ya zaɓi Sanata Barau don takarar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, sannan Sanata Salisu Mustapha ya mara baya.

Akawun majalisar ne ya bayyana nasarar da Jibrin Barau ya samu.

Tuni dai aka rantsar da
Sanata Barau a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa a majalisa ta 10.