Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa

Daga BASHIR ISAH

An zaɓi ɗan takarar Shugaban Majalisar Dattawa na Jam’iyyar APC, Godswill Akpabio, a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa.

Akpabio ya lashe zaɓen da ƙuri’u 63 inda ya doke Sanata Abdulaziz Yari wanda ya tsira da ƙuri’u 46.

Akawun Majalisar Tarayya, Sani Tambuwal, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen.

Tambuwal ya ce sanatoci 107 ne suka kaɗa ƙuri’a.

Sanata Ali Ndume ne ya zaɓi Akpabio don takarar Shugaban Majalisar, yayin da Sanata Adeola Olamilekan, daga Jihar Ogun, ya mara masa baya.