Hukumar EFCC ba ta cafke ni ba- Sanata Kwankwaso

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Tsohon gwamna jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin da ke cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa ta EFCC ta cafke shi.

Hakan na cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Sanata Kwankwaso ya fitar a yau Lahadi.

Ta cikin sanarwar dai, Kwankwaso ya ce, shi da kansa ne ya je ofishin hukumar domin wanke kansa dangane da wasu zarge-zarge marasa tushe da ake yi masa.

Kazalika ya ƙara da cewa, “Na ziyarci shalkwatar hukumar jiya Asabar domin bata bayanai, kuma na gana da jami’an hukumar ta EFCC na tsawon wasu sa’o’i.”

A daren jiya Asabar ne dai labarin cewa EFCC ta cafke tsohon gwamnan ya yaɗu a kafafen yaɗa labarai har ma da na kafafen sada zumunta.

In dai ba a manta ba, Jaridar Manhaja ta ruwaito cewa, a baya hukumar ta EFCC, ta gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a watan Satumba kan zarginsa da aikata almundaha, karkatar da dukiyar al’umma da kuma karkatar da kadarorin gwamnati ga wasu mukarraban gwamnatinsa amma ya gaza amsa gayyatar.