Marigayi Ahmed Abubakar: Ba rabo da gwani ba…

Daga ALIYU DANGIDA

Duk mai rai zai ɗanɗana zafin mutuwa, kuma ita mutuwa dole ce sai dai idan lokacin mutum ba zo ba, ta kan zo ta wata sila ko hatsarin mota, rashin lafiya ko wani ibtila`i ko mutum kwanan sa ya qare ba tare da jiyya ko wani ciwo ba.

Na zavi in yi wa abokin aikina, Marigayi Ahmed Abubakar wannan rubutu da hausa saboda waɗanda suka yi masa rubutun ta`ziyya dukkan su da harshen turanci suka gabatar, kuma a matsayina na mawallafin mujallar Hausa na ga ya dace in rubuta da Hausa.

Da farko dai, tunda na fara aiki jarida shekaru 22 da suka gabata a iya gani na da tunani ba, ban ga ɗan jaridar da ya rasu kuma ya samu rubuce-rubuce na taaziyya a kafafen sadarwa kamar Ahmed Abubakar, a ƙalla na ci karo da rubutu mai ɗauke da taaziyyarsa ya kai sama da na mutum goma. Wannan na nuni da irin kyawawan halaye da mu`amala da mutane da Ahmed ke da ita a lokacin ya na raye.

Mun haɗu da Mariyagi Ahmed a shekarar 2006 jim kaɗan bayan ya canji abokin aikinsa Hassan Karofi a matsayin wakilin jaridar Daily Trust a jihar Jigawa, a lokacin akwai ƙarancin gidajen kwana a babban birnin Dutse, ni kuma ban daɗe da gina gidana a Kano ba, don haka na maida iyalaina Kano sai dai in zo aiki in koma.

Sakamakon haka ya sa idan muka zo Dutse tare da Ahmed a motata sai mu kama ɗaki a otal ɗin 3 star saboda a lokacin suna yiwa `yan jarida ragin kuɗin ɗaki don haka duk lokacin da muka zo Dutse acan muke kwana, wani lokaci idan ba mu samu kuɗin ɗaki ba sai mu je masaukin ajiyar baƙi na gwamnatin jiha a bamu ɗaki da safe mu kama gaban mu. Haka muka yi ta zarya a motata duk lokacin da za mu zo aiki Dutse ko wani gari a cikin jihar Jigawa.

Ba zan manta ba, watarana muna tafiya zuwa Dutse wajen aiki, sai Marigayi Ahmed ya ce Dangida ni ma ina son sayen mota tunda naga kana harkar, ya za `ayi in mallaki mota amma bani kuɗi na ba su cika ba? na ce wannan ai ba matsala ba ce zan samo maka mota daga baya ka cika, haka aka yi kuwa, motar da Ahmed ya fara hawa ƙirar Golf 3 a waje na ya saye ta. A lokacin a otal ɗin Central wajen wani abokin manajan wurin muke ajiye ta sai mu tafi da tawa idan muka dawo sai ya ɗauki tasa ya tafi gida.

Wata rana marigayi yake ce mani wai kai Dangida da motar ka za mu ci gaba da zuwa Dutse, mu rinqa zuwa da tawa wani lokaci mana? amsar da na ba shi ita ce ai tawa sabuwa ce kai kuwa ta hannu ce mu ƙyale ta huta a zirga-zirga cikin gida, yayi dariya ya ce Dangida ke nan. Mun ɗauki tsawon lokaci muna wannan zirga-zirga da shi, amma haƙiƙanin gaskiya tunda nake da shi wani abun ɓacin rai ko gardama bai tava haɗa mu da shi ba, da ya fahimci bana shan mai saboda koda yaushe tankin motata a cike yake sai idan mun je cin abinci kafin mu gama ya biya, wani lokaci idan muka zo kama ɗaki shi yake biya mana.

Muna tsakar wannan zarya sai muka nemi gidaje daga hukumar gidaje ta jihar Jigawa kuma muka samu a rukunin gidajen janbulo wanda tsohon gwamnan Saminu Turaki ya gina gab da ƙarewar wa`adin mulkinsa a unguwar Takur. Gida na da na Marigayi ba nisa, haka muka zauna tare da ci gaba da hulɗa ta zumunci har Allah Ya sa aka zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban ƙungiyar manema labarai (Vice Chairman Correspondent Chapel) a jihar Jigawa har ya kai muƙamin shugaban ƙungiyar daga baya ya samu canji aiki zuwa Abuja muna gaisawa lokaci zuwa lokaci, idan na je Abuja na kan neme shi mu gaisa, har ta kai ga ya sake dawowa Jigawa da aiki.

A wannan lokacin ana neman wanda zai riƙe muƙamin shugaba a ƙungiyar lokacin wanda yake riqe da muqamin ya bar jihar, mutane da dama sun tuntuve ni da in fito in yi takara ta shugaba ko mataimaki, amma a lokacin na basu haƙuri tare da nuna masu bana buƙatar wani muƙami a matakin ƙungiyar manema labarai domin na yi a baya kuma na bada gudunmawa, na kuma nemi matakin sakatare a ƙungiyar `yan jaridu ta ƙasa reshen jihar Jigawa a zaɓen 2016 inda Allah bai yi zan samu ba tare da wasu daga cikin abokan aiki na da suka yaƙe ni amma bai dame ni saboda na san Allah ne bai rubuta zan yi ba.

Ana cikin wannan dambarwa saai Allah Ya dawo da Ahmed Jigawa don haka sai aka sake zaɓarsa ya zama shugaba, abinda zan ce akan marigayi Ahmed Abubakar mutum ne mai gaskiya da riƙon amana, yakana da son zaman lafiya tare da son ganin ci gaban duk wani da yake ƙarƙashinsa. Tabbas Marigayi mutum ne mai haƙuri da kawaici, haƙurinsa ya sa wasu ke ganin yana da rauni a harkar shugabancinsa duk da kowane shugaba ya kan tsinci kansa zagaye da mutanen kirki da na banza.

Haka ta kasance da rayuwar shugabancin Marigayi Ahmed amma wannan bai sa ya karkata da hankalinsa wajen waɗannan mutane masu ganin sun sa ya canja aƙidarsa ko kuma ya bi ra`ayinsu ba, akwai lokacin da idan ya ga hayaniya ta ƙi ci ta ƙi cinyewa ana ta ɗora masa laifi sai ya ce zai ajiye muƙamin, sai mu ce ka yi haƙuri shi shugaba ai juji ne duk sharar da aka kwaso shi ake jibgawa.

Kafin rasuwarsa Marigayi Ahmed shine wakilin jaridar ‘The Sun’ kuma mutum ne mai son zaman lafiya da kula da haƙƙin mambobinsa da iyalansa ban taɓa ganin yana waya da iyalinsa, abokin aiki ko wani na ƙasa da shi ka ji ya na ɗaga masu murya ba, hasalima idan yana waya ko kusa kake da shi ba lalle ka ji da wa yake magana ba. Ya kasance zakaran gwajin dafi wajen kare martabar dukkanin wani shugaba ko gwamnati duk lokacin da aka zo da wani labari wanda ba zai yiwa gwamnati daɗi ba, ya kan yi ruwa da tsaki wajen hana ayi labarin nan sai dai idan an bijire masa ba yadda zai yi.
Don haka samun shugabanci irin na

Marigayi Ahmed zai yi wahala musamman yadda aikin jarida a wannan lokaci ya taɓarɓare ba a ganin yan jarida da ƙima ga kuma rashin girmama juna da tarbiya saɓanin lokutan baya. Fatan mu shine Allah Ya kyautata makwancinsa, Ya Rahamshe shi, babu shakka Marigayin ya samu kyakkyawan yabo a wurin alumma da dama har ya zuwa yanzu nan da nake rubutun ban ji wani ya faɗi akasin alkhairin sa ba. Kuma Allah Ya sa halayensa na gari su bi shi cikin kabarinsa.

Dangida shi ne Mawallafin mujallun Mahangar Arewa da Hotpen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *