Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Hukumar Gudanarwar Kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi ƙarƙashin jagorancin Manajan Daraktanta Alhaji Abdul Bashir Husain bisa irin matakai da take ɗauka don kyautata cigaban kasuwar.
Gwamnan da Kwamishinan Yaɗa Labarai da al’amuran cikin gida Baba Aliyu ɗantiye ya wakilta a yayin ƙaddamar da kayan kwashe shara da hukumar kasuwar Muhammad Abubakar Rimi ta gudanar a harabar kasuwar ranar Alhamis.
Ya yi nuni da cewa kasuwanni wajen na tara shara saboda hada-hadar jama’a wannan mataki na samar da kayan shara yana da muhimmanci.
Ya ce kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi ta zama zakara gwajin dafi da ya kamata sauran kasuwanni su kwaikwayeta domin hakan taimakawa ƙoƙarin da gwamnati take ne wajen kauda shara.
Baba Halilu ɗantiye ya yi kira ga ‘yan kasuwa su baiwa wannan tsari haɗin kai da goyon bayan wajen kula da alkinta kayayyakin da aka samar don kyautata tsaftace kasuwar.
Shi ma a nasa jawabin, kwamishinan ayyuka na musamman Hon. Aliyu Yanmedi ya yaba wa tsarin na samar da kayan kwashe shara da manajan daraktan hukumar kasuwar ta Abubakar Rimi ya yi wanda ya ce hakan zai bada gudunmawa sosai ga tsaftar kasuwar.
Shi ma a nasa jawabin manajan daraktan Hukumar Kasuwar ta Muhammad Abubakar Rimi, Alhaji Abdul Bashir Husaini ya bayyana cewa ranar tarihi ce da farin ciki a gare su domin tun kafa kasuwar bata taɓa mallakar kayan shara kamar wannan ba.
Ya gode wa Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa sahalewa da ya yi aka samar da kayayyakin, inda ya yi kira ga ‘yan kasuwar da jami’an tsaro su sanya ido don kula da su a koyaushe.
Alhaji Bashir Abdul Husaini ya ce kayan da aka samar domin kulada tsaftace kasuwar ta Muhammad Abubakar Rimi sun haɗa da motocin ɗiiban shara guda Biyar da shebur da minjagara da tsintsiya da robobi da kowane mai shago zai ajiye a shagonsa na zuba shara da sauran abubuwa da dama.
A nasa jawabin daraktan mulki na hukumar kasuwar, Alhaji Nasiru Abdullahi mai Kano ya bayyana cewa kyakkyawan tunani na shugaban kasuwar na ganin an samu hanyar kawar da shara cikin sauri ta sa ya bijiro da wannan tsari wanda yakamata kowa ya bada haɗin kai domin cimma nasara.
Taron ya samu halartar mutane da dama da suka haɗa da shugabannin ƙungoyi a kasuwar da dattawa da sauran ‘yan kasuwa.
