Hukumar NFF na neman wanda zai zama kocin Flying Eagles

Spread the love

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bazama neman wanda ya cancanta domin zama kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta ’yan ƙasa da shekaru 20, wanda aka fi sani da Flying Eagle.

Sanarwar da NFF ta fitar ta ce, “Ga duk wanda yake neman zama kocin tagawar, to ya ziyarci shafin intanet na Hukumar – (https://thenff.com/job/ɓacancy-for-the-position-of-u-20-male-national-team-head-head) -coach/), ya saka duk bayanansa, sannan ya zama yana da aƙalla lasisin CAF B, dole ne kuma ya kasance a aikin horar da ƙwallon ƙafa na aƙalla shekaru biyar, ya kasance mai ƙwararre a wasannin cikin gida na Nijeriya, mai kyawawan halaye na jagoranci da kuma iya sadarwa yadda ya kamata cikin harshen Ingilishi.

“Haka zalika, ’yan takara dole su kasance masu gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukansu, su kasance a shirye da kuma son yin aiki tare da sashen fasaha na NFF da kuma ƙaramin kwamitin fasaha na NFF, dole ne su kasance sun samu nasarar koci a cikin shekaru uku da suka gabata kuma su kasance cikin shiri don yin aiki tare da shugabannin NFF.

“Ana gayyatar daga dukkan masu sha’awar horar da ‘yan Nijeriya, ciki har da waɗanda ke aiki a ƙasashen waje.

“Za a rufe da tsakar daren Lahadi, 4 ga Agusta, 2024, tare da wanda ya yi nasara da za a ba shi suna bayan cikakken tsarin tantancewa.”

Nijeriya ta gaza tsallakewa zuwa gasar AFCON ta U17, Flying Eagles sun yi muguwar rashin nasara a gasar kofin Afrika ta 2024 da aka yi a Ghana, inda suka faɗo a matakin rukuni

By ukarofi