Ina ma dai Malam Shekarau zai yi haka..!

Kowa ya san siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, siyasa ce mai dabaibaye da addini da tarbiyya. Don haka ma da dama al’umma ke kallon Malam Shekarau da ƙima kuma suke girmama ra’ayinsa, sannan suke bin sa ba don kuɗi ko mulki ba, sai don aƙida. Hatta lokacin da mulki ya suɓuce a hannunsa, akwai ’yan amanarsa da dama da suka cigaba da wannan azumin na rashin gwamnati, ba su bi wani ba, sun zauna da shi a yanayin akwai da babu.

Dawowar Malam Ibrahim Shekarau cikin jam’iyyar APC bayan ya bar PDP, wacce ya yi iƙirarin rashin adalci da danniya da rainin wayo da babakere da jam’iyyar ta yi masa na fifita tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, da ya zo a matsayin baqo a wannan lokacin zaɓen 2015 akan shi da ya jima a ciki, wanda wannan dalilin ya sa shi da magoya bayansa suka fice, masoya da yawa a APC suka shiga murna suka kuma cigaba daga inda suka tsaya na ladabi da soyayya da goyon baya. Ko da ya dawo APC, jama’a da dama a lokacin suna cikin fushi da rashin tabbas, amma ganin sa sai tsuminsu na aƙida ya motsa. Don haka suka dawo suka rungumi tsaginsa suka dafa aka kai gaci, wanda idan dai ba son zuciya mutum zai faɗa ba tabbas zai ce, ‘cin zaɓe a shekarar 2019, lallai da sa hannun Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa a Kano’.

A kakar zave ta bana ko ma dai mene ne, kowa ya san dangantakar Malam Ibrahim Shekarau da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Nasiru Umar Gawuna, al’ummar gari da ma ’yan siyasa, da na kusa da Gawuna da magoya bayan Sanata Shekarau kowa ya ji a ransa takarar Gawuna idan akwai wanda zai fara jin daɗi ya tallafi tafiyar, to shakka babu Malam Ibrahim Shekarau ne duba da Gawuna ɗan halaliyarsa ne na cikin gida a siyasacne.

Tun yana Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa har zuwa muƙamin kwamishina har ya kai matakin Mataimakin Gwamna ba a tava jin inda ya yi masa butulci ko ya kauce a tsarin Malam ba. Kai hatta haƙuri da juriya da kau da kai da biyayya duk ana ganin akwai irin nason zamansa da Malam Shekarau. A zamansa da Gwamna Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai tava yin butulci ba, yadda wasu ke yi wa iyayen gidansu su bi mai mulki ko ma su haɗu da mai mulkin su manta tsohuwar alaƙa, su yaƙi tsofaffin iyayen gidan nasu.

Malam Shekarau ya kamata ya rabu da neman makomarsa a siyasance, saboda tuntuni Allah ya zaɓa masa makoma a Kano, wacce ita ce, babu maigida a siyasance kamar nasa shi da Kwankwaso. Kai ma ka fitar da gwamna daga gidanka, wanda ka san mutumin kirki ne, wanda zai iya.

Manyan ’yan siyasa sun zauna a gida sun yi jagoranci kuma su na nan da martabarsu ba sai da suka shiga wata takara ba. Misali; Alhaji Musa Gwadabe ga su Imamu Wali ga Marigayi Alhaji Ammani Inuwa, su Alhaji Abubakar Rimi da sauransu. Duk wata makoma ta magoya baya za ka same ta ne idan ka haƙura da buƙatar kanka ka ɗaga hannun na ƙasa da kai har karansa ya kai tsaiko, musamman tunda dai ka san ba ɗan kunama ka goya wa baya ba.

Jama’a sun ɗauka ƙoƙarin da Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi na ba wa Gawuna takarar nan, Shekarau zai yaba, musamman da shi Malam Ibrahim Shekarau lokacinsa bai iya ba wa mataimakinsa takara ba, saboda tulin matsalolin da ke biyo baya, amma shi Ganduje ya zaɓi Dr Gawuna ya ba shi duk kuwa da ya san sun fi kusa da Malam Shekarau.

Ina ma dai Malam Shekarau zai yi haƙuri ya zauna a APC da shi aka kafata, gidansa ne, ta yaya za ka tsaya jin kiraye-kirayen wasu da za su kai ka su baro ka? Kada ka manta dai irin wancan hayaƙin da aka yi a baya yana nan, masu hali ba sa sake halinsu! Ba a sarki biyu a fada guda.

Ka san wannan karatun, Mai girma Malam Shekarau. Ina ma za ka zo ka dafa wa yaronka mai biyayya da juriya da haƙuri mai riƙon amana kai da magoya bayanka ya kai gaci a jam’iyyar APC, maimakon ɓallewa daga jam’iyyar, kuma idan Allah ya nufa ya ci ba sa hannunka, babu na mutanenka, me ka ke tunanin zai biyo baya? Bahaushe ya ce, “da babu dai, gara ba daɗi”, kuma “sulhu allheri ne”.


Don haka laifin wani kada a bari ya shafi wani. Allah ya huci zukatanka, ya kawo mafita, amin!

Bilkisu Yusuf Ali, Marubuciya kuma manazarciya ce a Kano.