Kasancewar mutane masu aƙidu da al’adu daban-daban na buƙatar haƙuri da mutunta juna

Daga FA’IZA MUHAMMAD MUSTAPHA

Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar da wani taro a jiya, albarkacin ranar adawa da kalaman kiyayya ta duniya, inda zaunannen wakilin Sin dake majalisar Zhang Jun ya yi kira ga ƙasashen duniya su mutunta tare da haƙuri da juna, kana su rika tattaunawa cikin adalci don yaki da kalaman kiyayya. Ƙasar Sin ta kasance daya daga cikin ƙasashen da suka gabatar da ƙudurin ayyana ranar ta yaƙi da kalaman kiyayya a shekarar 2021, inda aka fara gudanar da ita karon farko a bana.

Kamar yadda wakilin na Sin ya bayyana, yaƙi da kalaman ƙiyayya na bukatar kasashe su mutunta ’yanci da moriyar juna, da watsi da girman kai. Matukar da gaske ana son cimma zaman lafiya a duniya, to ya kamata gwamnati ta zama abar koyi ga jama’arta. Bai dace gwamnati ta rika yada ƙarairayi da zarge-zarge ba, domin jama’arta za su yi koyi da ita, lamarin da zai haifar da gadon kiyayya mara tushe tsakanin al’ummomi.

Misali, an ga yadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya riƙa danganta annobar COVID-19 da kasar Sin, lamarin da ya sa aka rika nuna kyama ga mutanen Sin da Asiya a ƙasar da sauran ƙasashen yamma. Ko a lokacin babban zaɓen ƙasar, irin furucinsa ne ya haifar da harin da magoya bayansa suka kai ginin majalisa ta Capitol a ƙasar.

Hakuri shi ne tushen zaman lafiya. Kasancewar mutane daban-daban, masu addinai da aƙidu da launi da al’adu daban-daban, na buƙatar haƙuri da mutunta juna. Hadin kan ƙasa da ƙasa don moriyar juna, cikin adalci da mutunta juna, zai iya tabbatar da zaman lafiyar da ake muradi.

Haka zalika shirye-shirye kamar irin na abota tsakanin matasan Sin da Afrika dake zaman dandalin musaya, zai yi gagarumin tasiri wajen kawar da rashin fahimtar dake haifar da kiyayya. A ganina, nan gaba, matasan Sin da Afrika da za su zama manyan gobe, za su kasance tamkar ’yan uwa ba tare da la’akari da bamban-bambacen dake tsakaninsu ba.

Irin wannan shiri da makamantansa, za su kawar da kyama da kiyayya don tabbatar da zaman lafiya da mutunci da kuma jituwa tsakanin al’ummomi. Wannan, shiri ne da ya kamata sauran ƙasashe su yi koyi da shi yayin da ake ƙoƙarin kawar da kiyayya a duniya.