Takardar da ta tona ƙarairayin Amurka

Daga CMG HAUSA

A ƙarshen watan Mayun da ya gabata, sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Antony Blinken ya gabatar da wani jawabi a kan manufofin ƙasar Amurka a kan kasar Sin, inda ya sha tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin da ma shafa wa ƙasar bakin fenti a kan manufofinta na gida da waje.

Sai dai kome ƙoƙarinta, ba ta iya boye ainihin burin da take neman cimmawa na daƙile ci gaban ƙasar Sin daga dukkan fannoni ba. A ranar 19 ga wata da dare, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fitar da wata takarda mai taken “Kura-kurai da ke tattare da ra’ayin Amurka game da ƙasar Sin da ma ainihin gaskiyar abubuwan”, inda ta fallasa “yadda yaudara, munafunci da hadarin dake ƙunshe cikin manufofin Amurka game da ƙasar Sin” tare da cikakkun bayanai da kuma alƙaluma.

Wace ce ke lalata tsarin ƙasa da ƙasa? Wace ce kuma ke keta haƙƙin dan Adam a sassan duniya da ma satar sauraron ƙusoshin ƙasa da kasa? Wannan takarda mai ƙunshe da dogon bayani ta zayyano kura-kurai da ma ƙarairayi kimanin 21 da ke tattare da manufofin ƙasar Amurka a kan ƙasar Sin, ta kuma samar da cikakkun bayanai da alƙaluma don faɗakar da kasashen duniya a kan yadda ƙasar Amurka ke haifar da rikici ga duniya, da kuma tilastawa wasu ƙasashe su bi tsarinta a harkokin diplomasiyya, da ma yadda ta fi kowace ƙasa a duniya wajen lalata haƙƙin dan Adam da kuma kai hare-hare ta yanar gizo.

Daga cikinsu kuwa, furucin ’yan siyasar Amurka dake cewa wai “Sin na haifar da ƙalubale mafi tsanani ga tsarin ƙasa da ƙasa” na daga cikin munanan ƙarairayi da suka yi, kuma abin dariya ne yadda suka furta cewa, wai “Amurka na kare dokoki da yarjejeniyoyi da ƙa’idoji da ma hukumomi na ƙasa da ƙasa.”

Ban da haka kuma, ƙasar Amurka tana kuma ƙoƙarin kafa “tsarin tattalin arzikin Indo-Pasifik”, a yunkurin kafa tsarin ƙa’idojin ciniki da ke ƙarƙashin jagorancinta, tare da tilasta ƙasashen shiyyar da su katse hulɗar ciniki da ƙasar Sin. Tsarin wanda ke kare moriyar Amurka, ya kuma haddasa cikas ga farfaɗowar tattalin arzikin duniya bayan annoba.

Kome ƙoƙarinta, Amurkar ba za ta iya boye burin da take neman cimmawa na daƙile ci gaban kasar Sin da kuma neman shimfida tsarin yin babakere a duniya.

Fassarawa: Lubabatu