Kotu ta ayyana ranar shari’ar NDLEA akan Abba Kyari

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana ranar 26 ga Fabarairun 2026 domin yanke hukunci a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Sha Raya Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta shigar akan tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DCP Abba Kyari.

Mai Shari’a James Omotosho ya bayyana haka ne a jiya Juma’a bayan lauyoyin NDLEA da na Kyari da ‘yan uwansa sun gabatar da takardun kare kansu da muhawarar karshe a gaban kotu.

Kyari tare da ‘yan uwansa guda biyu, Mohammed Kyari da Ali Kyari, na fuskantar tuhume-tuhume guda 23 da NDLEA ta shigar na zargin su da ƙin bayyana dukiya, ɓoye mallaka, da kuma juya wasu kuɗaɗe da ake zargin sun fito daga haramtattun hanyoyi.

A cewar NDLEA, hukumar ta gano dukiyoyi 14 da ake alakantawa da Kyari, ciki har da manyan shaguna, gidaje, filayen polo, gonaki da sauran filaye a Abuja da Maiduguri.

Haka kuma, hukumar ta ce ta gano Naira miliyan 207 da Euro 17,598 acikin asusun bankin Kyari.

Saidai Kyari ya musanta tuhumar, yana mai cewa ya bayyana dukiyar sa da ta matarsa bisa ga abin da doka ta tanada.

Ya kuma ce wasu daga cikin kadarorin da NDLEA ta yi ikirari mallakinsa ne, nasa marigayi mahaifinsa ne wanda ya bar yara sama da 30.

By Babaji