Kotu ta ba da umarnin tsare Babban Hafsan Sojoji, Faruk Yahaya

Daga WAKILINMU

Wata Babbar Kotu mai zamanta a Minna, babban birnin Jihar Neja, ta ba umarni kamo Babban Hafsan Sojoji, Janaral Faruk Yahaya bisa zargin cin mutuncin kotun.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Halima Abdulmalik ce ta ba da wannan umarni.

Kazalika, umarnin kamun ya shafi har da Manjo Janar Stevenson Olugbenga Olabanji.

Alkali Halima wadda ita ce alƙalin-alƙalan jihar, ta ce buƙatar kamo Yahaya ta taso ne sakamakon wata shari’a da ke gabanta.

Kotun na buƙatar a kamo Yahaya da Olabanji a ajiye su a Gidan Gyaran Hali na Minna saboda rashin bin umarninta a ranar 12 ga Oktoban 2022.

Ta ce a tsare su biyun da ake zargin har sai sun yi wa umarnin kotun biyayya.

Daga nan, ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ran 8 ga Disamba, 2022.