Tarin kura-kurai a littafin ‘Halayyar Zamani’

Daga SANI AHMAD GIWA

Littafin ‘Halayyar Zamani’ ɗaya ne daga cikin jerin littafan Adabin Kasuwar Kano, mai ɗauke da shafuka 148, wanda suka haɗu suka ja zaren labarin. Fa’iza S. Muhammad ce ta ƙaga labarin, inda maɗaba’ar Megacraft wadda ba a bayyana adireshinta ba ita ta wallafa shi, farashin da ake fansar shi a kasuwar littafai Naira 300 ne kacal.

Bayan fansar wannan littafin a kasuwa, abin da zai biyo baya kuwa ai sharhin bayan karatu ne, a yunƙurin ya Allah ko dai yabo ko suka mai ma’ana a kan yadda manazarci ya ga littafin, ya kuma kalle shi, ko ba komai domin marubuciyar ta san ko wace irin alƙibla za ta dosa a rubutunta na gaba. Don haka ba luguden littafin wannan marubucin zai yi ba, kamar yadda kuma ba baje shi zai yi a faifai ba, domin fitar da tsaki da tsakuwa tare da cin tsutsa.

A’a, ba kuma manufar wannan sharhin ba ne a yi wa littafin nazarin kokwanto. Dalili kuwa wannan shi ne littafin ta na farko da ta wallafa, don haka tana buqatar uzuri. Sai dai ta lura ba ta makara ba duk da kasancewarta ‘sabuwar yankan rake’ ce a duniyar rubutu da marubuta.

A kan wannan mai sharhin zai dai yi ƙoƙarin fahimtar da ita cewar Borno Gabas take. Amma bari mu yi tattaki mu leƙa mu gani mene ne na ci, da na zubarwa a ciki!

‘Halayyar Zamani’, labari ne mai fuska ɗaya, inda marubuciyar take ƙoƙarin bayar da labarin wata mata mai suna Fatima wadda ita ce babbar tauraruwar labarin, wacce ta fuskanci ƙalubalen rayuwa tun kafin ta faɗo duniya har zuwa haihuwarta, wato ta fuskanci tsangwama da mummunar ƙiyayya da tsana wurin kishiyar mahaifiyarta wato Inna Jummai. Babban ƙalubalen da Fatima ta fuskanta a rayuwarta shi ne yadda Ɗanliti ya ci zarafinta ta hanyar yi mata fyaɗe.

A sakamakon haka ne kuma Fatima ta samu damar yin kyakkyawar rayuwa daga baya, har ta kai ga ta samu ingantaccen ilimi da murza sitiyarin manyan motoci sakamakon haɗuwarta da wani bawan Allah da ya zama da ita tamkar ɗiyar shi ta ciki a Kaduna, haka Fatima ta zama jinin wannan bawan Allah, duk abinda ya yi wa ‘ya’yan shi su Zainab da Fatima da Rukayya ita ma an yi mata.

Da ƙarshe dai Fatima wacce ta mori miji mai kyautata mata da sauke haƙƙin iyali, ya gina mata babban asibiti da kuma ba ta goyon baya na kafa ƙungiyar mata masu rajin kare haƙƙin matan da ake yi wa fyaɗe.

Bari mu tsaya a nan sai mu tsakuro tarin kura-kuran da sabuwar marubuciyar ta yi zubar-gadonsu wanda za mu iya cewa sun zarce lissafin Ras-Kwana.

Tun da farko marubuciyar littafin ba ta yi amfani da salon sarrafa harshe ba yayin rubuta littafin musamman wajen yin karin magana ko tagwayen kalmomi ko amfani da siffatau kai tsaye (Personification) ko siffatau mai-kama (simile) ta saki rubutun sakaka, babu gishiri bare magi, haka yake a salamce.

Kwata-kwata marubuciyar ba ta yi amfani da dokar bin ƙa’idojin rubutu ba, babu alamar waqafi ko tsayawa ko alamar tambaya bare kuma uwa uba alamar motsin rai, duk da akwai wurare da dama da ya kamata marubuciyar littafin ta yi amfani da su. Wani abin lura kuma, tun daga farkon littafin har zuwa ƙarshe babu inda marubuciyar ta yi amfani da alamar nuna maganar wani.

Marubuciyar littafin ba ta yi amfani da dabarun jan ra’ayin mai karatu da wasa ƙwaƙwalwarsa ba wajen yin waiwaye (Flash back ko Foreshadowing) don riƙe mai karatu ya ji littafin bai gundurarwa.

Duk da marubuciyar ta yi amfani da jigo ɗaya ne tal, amma ta kasa ɗora tsinin alƙalami ta gina labari mai sarƙaƙiya da kawo maslaha a ƙarshe kamar dai yadda ta kama kame-kame sai dai a ce wane ɗan gidan wane ya yi wa wance fyaɗe, ko kuma an ji labarin an kama Ilan Mai Unguwa ko mun dawo gaisar da ‘yar ajinmu an yi mata fyaɗe, shi ke nan.

Jigon da marubuciyar ta ɗauka jigo ne mai matuƙar muhimmanci, amma kuma alƙalamin marubuciyar ya yi gardamar rubuta abubuwan da za su gamsar da mai karatu ya tabbatar da littafi ne ya ke karantawa ba jagwalgolo ba. Haka nan idan za a auna littafin a sikeli ne ko kusa ba zai samu ko kashi talatin cikin ɗari ba.

Ni dai da na karanta wannan littafi ciki da wajensa, zan iya kiran wannan aikin da aikin baban giwa, saboda tamkar vata itace ne wajen dahuwar ƙaho.

A shafi na 13 marubuciyar ta rubuta ‘Maƙarfi ƙaramar hukumar Kaduna, maimakon Ƙaramar Hukumar Maƙarfi, Jihar Kaduna; sai kuma a shafi na 14 marubuciyar ta ce Ilan Mai Unguwa ya yi wa yara fyaɗe har wasu sun mutu.

A haka marubuciyar ta kasa kawo hovvasar da mutanen unguwa suke yi tare da hukuma don ganin an hukunta shi, amma yana ta yawon shi yana shan iskar Subhana duk a cikin garin Maƙarfi da suka kwankwaɗi ilimin zamani da kuma wayewa.

A shafi na 16 da 17 da 18 marubuciyar ta yi tashin-gauron-zabi ko tsallen-baɗake wajen zura labarin iyayenta da kuma na Inna Jummai da yaron ta Ɗanliti, sannan ta saki labarin ta koma faɗakar da mai karatu ba wacce ake bai wa labarin ba.

Allah Sarki rubutaccen Adabin Hausawa yana cikin tsaka-mai-wuya! Idan dai har marubuciyar littafin Halayyar Zamani za ta kasa rubuta farkon sunan Fatima da Maryam da Rukayya da Zariya da Maƙarfi da Kaduna da Zainab da Mustafa tare da Yasmin da babban baƙi, ai ya kamata sunan Mai Duka (Allah) a rubuta shi da babban baƙi, haka marubuciyar ta dinga rubuta sunan Allah tun daga farkon littafin har zuwa ƙarshen shi da ƙaramin baƙi.

Haka kuma a shafi na 41 marubuciyar ta nuna cewa Fatima ‘yar shekara bakwai ba ta san mece ce mutuwa ba, shin a wane ƙarni?

A shafi na 51 marubuciyar ta ce: “Aka yi assembly aka fito da hedimasta daga shi sai gajeren wando yana sussunkuyar da kai….” A wane gari ko a wace ƙasa hakan ke faruwa? Sannan a shafi na 52 ma ta bada labarin cewa jarumar littafin wadda ba a cika bayyana sunanta ba, ta ce hedimastansu ya yi niyyar yi mata fyaɗe amma ta janyo kwalba ta buga mishi. Anya irin biyayya da girmamawa zai sa ƙaramar yarinya ‘yar shekara sha biyu ta yi dubarar hakan? Tambaya ce ga marubuciya.

Duk dai ba mu bar shafi na 52 ba, inda marubuciyar ta ce: “Idan kuma mutuwa kika yi sai ya ɗauki gawar ya kai ki kogi….” Ma’ana idan ya gama amfani da ƙaramar yarinya har ta kai ga mutuwa sai ya ɗauki gawar ya kai kogi.

To wace hanya yake bi wajen fita da gawar daga ofishin sa ba tare da an gan shi ba? Gaskiya da sake wai an bai wa mai kaza kai. Sannan kuma duk a cikin Birnin Zazzau mai daɗaɗɗen tarihi wajen ilimi da wayewar kai hakan ta faru.

A shafi na 56 marubuciyar ta yi tuya ta manta da albasa, domin har iyayen Fatima da Rukayya waɗanda suka samu cikakkiyar tarbiyya suka gama ja musu kunne da nasiha lokacin da aka kai su makarantar kwana mai karatu bai ji inda aka musu huɗubar cewa su kula da addini sosai ba a matsayinsu Musulmai.

A shafi na 63 marubuciyar ta nuna yadda Inna Jummai take ɗora yaronta Ɗanliti kan ɗabi’ar ya illata Fatima ɗiyar mijinta, ya gurɓata rayuwata ta hanyar yi mata fyaɗe. Wannan manazarcin zai miƙa tambayar shi ga sabuwar marubuciyar ‘Halayyar Zamani’, shin wannan adabin malam Bahaushe ne ko adabin Yahudawa? A ƙasar Hausa uwa da kanta ta ingiza yaronta ya aikata fyaɗe?

A shafi na 71 kuma cikin littafi na biyu marubuciyar ta kasa yin amfani da hukuma ko jami’an tsaro wajen dasa zargi da bincikar Ɗanliti da Rukayya qawar Fatima don a rikitar da ƙwaƙwalwar mai karatu, kawai sai ta bar su salin-alin suka kama harkokinsu a gari ba wanda ke zarginsu.

Bugu da ƙari a cikin shafi na 83 mawallafiyar ta yi ƙememe ta kasa nuna kuskure da sakacin iyayen da har za su bayar da ɗiyarsu ‘yar shekara uku kacal wani tsoho mai shekara fiye da hamsin ya tafi da ita har gidan shi sannan ya yi mata fyaɗe har ta baƙunci ƙiyama.

Duk a cikin littafi na biyu shafi na 84 marubuciyar ta bayyana cewa tsohon da ya yi wa ‘yar shekara uku fyaɗe da yake kora bayani a gaban alƙali dalilin da ya sa ya aikata hakan sai ya ce sharrin sheɗan ne, har wani ɗan sanda yana buga mai kulki. Tambaya ga mawallafiya, da ma ɗan sanda ko wani jami’i yana da hurumin yin wani hukunci lokacin da alƙali ke shari’a?

Wani kuskure da mawallafiyar ta tafka a shafi na 92 shi ne yadda take bayar da labarin lokacin da Fatima za ta rubuta jarrabawar shiga jami’a wato JAMB, zaɓinta na farko ABU inda take son karatun lauya, sai zaɓi na biyu kuma Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato, inda a nan kuma take son karantar fannin likitanci, sa’ilin da ta samu sakamakon jarrabawa har kusan ɗari biyu da talatin, hakan ya sa ta samu Jami’ar Ɗanfodiyo.

Tambaya ga marubuciyar ita ce shin wane fanni tauraruwar littafin ta karanta lokacin da take makarantar sakandaren kwana da ke Soba, kuma yaushe hukumar JAMB ta fara amincewa da wannan tsari irin na Fatima? Saboda ya haramta duk jami’o’in ƙasar nan su ba ta takardar shiga jami’a a dokar hukumar JAMB.

Idan kuma muka waiwaya baya cikin shafi na 62, an bayyana Rukayya kawar Fatima ta karanta fannin kasuwanci ne da masana’antu a sakandare ɗin ta, me ya sa a cikin littafi na biyu marubuciyar ta ɗora ta a matsayin malamar asibiti?

Kamar yadda marubuciyar ‘Halayyar Zamani’ ta bayyana a shafi na 95 cewa Anti Zainab da mijinta sun kawo mata ziyara a makaranta har ta na shiga da su cikin ɗakunan kwanansu, shin a Jami’ar Ɗanfodiyo maza suna shiga ɗakunan kwanan mata? Wannan mai karatu zai so ƙarin haske.

Sannan haka kawai a shafi na 96 marubuciyar ta nemi yin wasa da hankalin mai karatu inda ta ce an yi wa wata mai suna Maryam fyaɗe lokacin da ta fita an so hand-out cikin dare a wani ɗakin kwana, abin tambaya a nan shi ne; a ina aka yi fyaɗen, shin Maryam ɗakin kwanan maza ta je ko na mata, sannan ina jami’an tsaron Jami’ar Ɗanfodiyon suke?

A shafi na 103 marubuciyar ta yi gugar zanar bayyana jami’ar karatu a matsayin farfajiyar zama kara zube babu doka, inda ta ce wasu gungun matasa sun yi wa wata yarinya fyaɗe a cikin jami’ar kuma har da hura usur don sauran su bayyana, ko ina mawallafiyar ta voye masu gadin jami’ar har suka kasa bayar da cikakken tsaro ga ɗalibai?

Idan muka shiga cikin shafi na 110 kuwa muka ɗan tsakuro nan wurin: “Bayan an sa ta a makara na ɗauko Ƙur’ani izufi sittin na durƙusa a gabanta na fara daga Baƙara sanda na kai Suratul Maryam, sannan na fara jero addu’o’i….”

Kokwanton da wannan manazarcin yake yi anya marubuciyar ta san hizifi nawa ne daga Bakara zuwa suratul Maryam kuwa? Ko tana nufin sai an jira Fatima ta yi wa gawar takwararta tilawa sannan za a yi mata sallah? Ko kuwa karatun yaya Mustafa masu jiran a fito da gawa za su tsaya saurara?

Kafin in ci gaba da lulawa cikin littafi na biyu, ya kamata makarancin wannan sharhin ya fahimci cewa ba luguden littafin ake yi ba kamar yadda na bayyana tun a farko, a’a hasalima marubucin ya yi alimbon fitar da wake a cikin garin masara, sannan bugu da ƙari manufar wannan sharhi don a samu gyara a wallafe-wallafen marubuciyar nan gaba, wannan ke nan.

Tun daga farkon littafi na ɗaya har zuwa ƙarshen na biyu, manazarcin littafin zai kasa fahimtar irin Hausar da marubuciyar ta yi amfani da ita, domin sun yi hannun riga nesa ba kusa ba da daidaitacciyar Hausa, kuma ba ta yi kama da Hausar Kano, Katsina, Sakkwato ko Zariya ba, sannan ba za a kira ta da Hausar Zamfarawa ko Hadejawa ba, ba kuma za a kira ta da Hausar baƙon haure ba. Kodayake ilimi kogi ne ba mu sani ba ko wata karɓaɓɓiyar Hausar ta bayyana!

A cikin shafi na 114 sabuwar marubuciyar ta ce bayan bikin ƙawarta Rukayya wadda aka kai Unguwar Rimi cikin birnin Kaduna, da wata biyu sakamakon jarrabawarsu ya fito, aka sa ranar da za a yaye su a jami’a, sannan za a rarraba kyautuka ga waɗanda suka yi ƙoƙari, sannan a faɗi inda aka tura su zuwa bautar ƙasa. Shin da ma haka ake yi da sakamakon jarrabawa ya fito sai makaranta ta tura mutum bautar ƙasa?

A shafi na 115 kuwa marubuciyar ta yi ƙoƙarin saka tauraruwar yin kiɗa bashi, ko wuce makaɗi da rawa, inda ta ce wa Anti Zee lokacin da take amsa wayarta cewa su yi wa tsohon hukunci daidai da shi, ka da su rage mishi. A matsayin Anti Zee lauya shin ita ce ke da alhakin yanke hukunci ko alƙali?

Duk a cikin tarin kura-kuran da suke jibge a cikin sabon littafin, za a ga wuraren da marubuciyar ta yawaita maimaita wannan maganar a cikin shafuka mabanbanta: “Wa’inda suke cewa sai da haɗin kan mace ake mata fyaɗe, su kuma ƙananan yara da ake musu su ma da haɗin kansu ne?

A cikin shafi na 117 marubuciyar ta kasa bayyana kwanakin da su Fatima da yaya Mustafa suka yi a Zariya da Maƙarfi sai dai kawai mai karatu ya ji cewa za ta koma wurin aikin bautar ƙasarta can Adamawa.

A shafi na 123 kuwa marubuciyar ta bayyana Fatima ta na off, ma’ana tana jinin al’ada, kusan har tsawon wata biyu kamar yadda ta nunawa sabon angonta. Kawai sai marubuciyar ta kasa nunawa mai karatu yadda angon nata ya nuna damuwarsa a cikin kwanaki sittin suna kwana gida ɗaya, kuma Mustafa ya kasa nusar da ita zuwa ga asibiti don duba lafiyarta.

Fa’iza S. Muhammad a cikin littafin nata ta yawaita nuna Yaya Mustafa zai zo Nijeriya akan dalilin da bai taka kara ya karya ba a cikin ‘yan awannin da aka sanar da shi wani al’amari ba tare da bayar da uzurin kwana ɗaya zuwa biyu ba.

Mawallafiyar ta ce matasa suka yi wa Ɗanliti dukan tsiya cikin dare kuma suka yanke gaban shi a shafi na 131, can a shafi na 147 kuma marubuciyar ta nuna cewa wasu matasa sun kama Ɗanliti a cikin wani kango suka yi mishi duka sannan suka ƙwaƙule mishi idanuwa da kuma wasu sassa na jikinsa. Shin marubuciyar ta na nufin duk lokacin da Ɗanliti ya ɗauka ba tare da gaba ba, ya ci gaba jinyar kansa a haka salim-alim.

Bangon littafin ‘Halayyar Zamani’

Tun daga farkon labarin da Fatima ta ke ba Maryam har zuwa ƙarshe babu inda marubuciyar ta yi ƙoƙarin nunawa mai karatu yadda Maryam ke ji yayin da ake ba ta labarin, musamman halin tausayi, mamaki, jin haushi ko razana bare kuma har a nuna Maryam ta yi wa Fatima tambaya.

Idan muka leƙa shafi na 140 zamu ga yadda marubuciyar ta yi riga malam shiga masallaci, inda ta yi saurin bayyanawa mai karatu dalilin da ya sa Mustafa mijin Fatima ke fushi da ita bayan bai fada mata dalilin ba.

A shafi na 146 kuwa mawallafiyar ta ce Inna Jummai ta samu hatsari wanda hakan ne ya yi sanadiyyar yanke ƙafafuwanta, daga bisani kuma mijin ya yi mata saki uku. To mai karatu zai so sanin wurin da Fatima suka haɗu da ita a ƙarshe har take yi mata alheri?

Nazartar littafin tun daga farko har zuwa ƙarshen sa, mai karatu zai ga babu inda marubuciyar ta ambaci sunan ƙasar da Mustafa mijin Fatima yake aiki.

Duka baya ga waɗannan matsalolin, littafin ‘Halayyar Zamani’ da marubuciyar ta raɗa wa suna ko kaɗan bai ci sunan shi ba, littafin ya saki linzamin shi tun farkon farawa.