Kotu ta haramta wa EFCC bincikar Bello Matawalle da jami’an Gwamnatin Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A. B. Aliyu, ta haramta wa hukumar EFCC gayyata ko tsare tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle.

Alƙali Aliyu ya yanke hukuncin haka ne yayin zaman Kotun a ranar Laraba, 31 ga Mayu, 2023, biyo bayan ƙarar da Farfesa Mike Ozekhome, SAN, ya shigar mai lamba FHC/GS/CS/30/2021 BETWEEN THE GOVERNMENT OF ZAMFARA STATE & 1 ANOR V. EFCC & 1 ANOR, a madadin Gwamnatin Zamfara.

Ya shigar da ƙarar ce inda yake ƙalubalantar hukumar EFCC game da gayyata, ko tsarewa, ko riƙewa, ko bincikar jami’an gwnatin jihar dangane da yadda aka tafiyar da kuɗaɗen jihar wanda Majalisar Dokokin Jihar ta kasafta.

Wanda a cerwar ƙarar Majalisar Dokokin Jihar da Babban Jami’in Bincike na Jihar kaɗai doka ta bai wa hurumin aiwatar da haka.

Da yake yanke hukuncin, Alƙali A. B. Aliyu ya ce EFCC ba ta da hurumin yin bincika a kan yadda aka raba kuɗaɗen Jihar Zamfara, haka ma ba ta da damar gayyatar jami’an Gwamnatin Jihar game da yadda aka tafiyar da kuɗaɗen jihar wanda Majalisar Dokokin Jihar ta raba.

Kotun ta ce, binciken da EFCC ke ƙoƙarin gudanarwa wanda har ta kai ga miƙa wasiƙar gayyata ga jami’an Gwamnatin Jihar Zamfara don su zo su amsa tambayoyi a kan yadda aka kashe kuɗin shigar jihar ko kuɗaɗen gwamnatin jihar.

Hakan a cewar Kotun, yunƙurin shiga hurumin da ba nata ba EFCC ɗin ta yi. Ta ƙara da cewa, wannan aiki ne da ya rataya a kan Majalisar Dokokin Jihar da Atoni Janar na Jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *