Kotu ta haramta wa Ganduje kusantar Filin Wasan Golf na Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Jihar Kano ta nuna wa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje yatsa bisa yunƙurin da gwamnatinsa ke yi na ganin ta tsaga tare da cefanar da Filin Wasan Golf mallakar jihar.

Manhaja Blueprint ta ruwaito cewa, Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, ta buƙaci kada wani mai ruwa da tsakin da ya kusanci wannan fili har sai lokacin da Kotun ta ayyana a matsayin ranar da za a dawo don ci gaba da sauraron ƙarar, wato ranar 5 ga Yuni bayan kuma an rantsar da sabon gwamnan jihar.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi niyyar ganin gwamnatin ta yi nasarar tsaga tsohon filin wasan mai daɗaɗɗen tarihi wanda a cikinsa jirgin sama na farko ya sauka a yankin ran 1 ga Nuwamban 1925.

Shi dai wannan fili da ake magana an samar da shi ne a shekara ta 1903 a lokacin Turawan mulkin mallaka, kuma an fara buga wasa a cikinsa ne a 1908.

A bayanan da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta aike wa manajojin wannan filin wasa na nuni da cewa an samar wa filin sahilewa ne a 1979 da zimmar shekaru 40 da suka bayyana wa’adin ya kare ran 6 ga Afrilu, 2019.

“Da wannan na ke sanar da ku cewa wa’adin da aka ɗiba ma wannan filin ya ƙare kamar yadda aka sa hannu, wato daga 6 ga watan Afirilun 1979 zuwa 6 ga watan afirilu 2019, a wata takarda da ke ɗauke da sa hannun Ibrahim Na Abba wanda gwamnan suka gabatar.”

Wannan matakin ya biyo bayan shigar da ƙarar da hukumar da ke kula da filin wasan ta yi a ran 29 ga Maris, 2023, inda ta ke karar gwamnatin jihar kano bisa yunkurin ta na keta filin wasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *