Shugabancin Kano: Ba zan biya bashin da ban ci ba, cewar Gwamna mai jiran gado ga Gwamna mai barin gado

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ƙin amincewarsa wajen biyan bashin da gwamnati Gwamna Abdullahi Ganduje ta ciyo bayan bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a kwanan baya wnda Hukumar Zaɓe, INEC, ta tabbatar masa.

Manhaja Blueprint ta rawaito cewar Abba Kabir, ya yi zargin gwamnatni mai barin gado ta ciyo basussuka da dama domin gadar wa gwamnati mai jiran gado.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya miƙa wa manema labarai a daren da ya gabata.

A cewar sanarwar, “Duk wani bashi ko lamuni da gwamnati mai ci ta karɓa daga bayan zaɓe zuwa yanzu, gwamnati mai jiran gado ba za ta biya shi ba matukar ba a sanar da zaɓaɓɓen gwamnan ba.”

Sanarwar ta Kuma tabbatar da cewa gwamnati mai jiran gado za ta bibiyi duk wasu sharuɗɗa da gwamnati mai barin gado ta bi wajen karɓo bashi daga masu bada bashi da lamuni na gida da waje.

Wannan Sanarwar dai ita ce ta biyu da gwamnati mai jiran gado ta fitar, tun bayan da Hukumar Zaɓe (INEC) ta miƙa wa Abba Kabiru Yusuf shaidar lashe zaɓen Gwamnan Kano a makon jiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *