Kuɗin da aka ware don yaƙi da labaran ƙarya sun yi kaɗan – Lai Mohammed

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labaru da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kuɗaɗen da ake ware wa ma’aikatarsa sun yi kaɗan wanda kuma ke kawo cikas wajen yaƙi da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a gaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dattawa domin kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa a 2023.

Ya ce ma’aikatarsa na buƙatar kuɗaɗe da ya kamata domin yaƙi da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci.

“Idan akwai ma’aikatar da ya kamata a ware wa kuɗaɗe da yawa, to ita ce ma’aikatar yaɗa labaru,” inji Lai.

Ya ce duk da cewa an yi watsi da gargaɗin da Amurka ta bai wa ‘yan ƙasarta a Nijeriya kan batun rashin tsaro a Abuja, amma ba a yi hakan ba yadda ya kamata na ganin hankalin ‘yan Nijeriya ya kwanta.

Ya kuma ce abin damuwa shi ne duk da cewa an ware wa ma’aikatar Naira biliyan 2.5 a matsayin kuɗaɗen kashewa a 2022, kashi ɗaya bisa uku na kuɗin shi aka sake ware mata na shekarar 2023 wanda kuma ya kai Naira miliyan 869.

By Editor