Zamfara SUBEB ta kashe sama da Naira miliyan 300 a ayyuka 65 a makarantun Ƙaura Namoda

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta hannun Hukumar Bayar da Ilimi Matakin Farko ta jihar ta aiwatar da ayyuka sama da sittin da biyar a makarantun firamare daban-daban da ke faɗin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke jihar.

Sakataren ilimi na Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda, Hamzat Aliyu ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da Blueprint Manhaja a ofishinsa a ci gaba da rangadin tantance fannin ilimin ƙananan hukumomin wanda hukumar ta ZSUBEB ta shirya a ranar Talata.

A cewarsa, hukumar bayar da ilimin farko ta jihar ta kashe sama da Naira miliyan 350 domin gudanar da ayyukan tsakanin shekarar 2019 zuwa yau.

Ya ce ayyukan sun haɗa da gyaran makarantu gaba ɗaya, gina ƙarin sabbin ɗakunan karatu, samar da ingantattun kayan koyarwa da dai sauransu.

Sakataren zartarwa ya buƙaci gwamnatin Jihar Zamfara da ta ɗauki qarin malamai a makarantun firamare ba kawai a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda ba har ma a dukkanin ƙananan hukumomi 14 na jihar.

A cewarsa, rashin isassun malamai a makarantun firamare a jihar ya kasance babban cikas da ya shafi tsarin ilimi matakin farko a jihar.

“Ina kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da hukumar kula da ilimi bai ɗaya ta jihar kan buƙatar da ke akwai na ɗaukar ƙarin malamai domin bunƙasa ilimin boko da kuma tsarin koyo da koyarwa kasancewar muna fuskantar ƙarancin malamai ta wannan fanni a jihar,” ya ce.

Hamzat ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Zamfara da hukumar kula da harkokin ilimi na bai ɗaya na jihar kan tallafin da suke bai wa ɓangaren ilimi a ƙananan hukumomi.