
aga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
A cigaba da ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da inganta rayukan iyalan ƴan sandan da suka rasu a bakin aiki, Kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara, CP Muhammad Dalijan ya miƙa wa iyalan jami’an ƴan sanda da suka rasa rayukansu a bakin aiki a jihar cakin kuɗi da adadinsa ya kai sama da Naira miliyan 29.
Kwamishinan, ya samu wakilcin Mataimakinsa, mai kula da harkokin kuɗi da mulki, DCP Salisu Bello Fago ne a wajen taron a hedikwatarsu ta jihar da ke Gusau, a yau Litinin.
Ya ce waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da; masu inshorar rai na Group, da waɗanda suka samu haɗari da kuma na ƙarƙashin shirin samar da walwala na Sufeton Janar na ƙasa.
Ya ce, shirin yana gudana ne a ƙarƙashin ofishin Sufeto Janar na jami’an ‘yan sandan Najeriya.
Ya ƙara da cewa, su na fatan matakin zai ɗore inda ya ce ba da jimawa ba za a bai wa kashi na gaba nasu rabon don suma su samu cin gajiyar shirin.
Kwamishinan ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen da aka ba su ta hanyoyin da suka dace.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Malam Ihsan Bashir, ya yaba wa babban sufeton ƴan sanda da kwamishinan bisa tallafin tare da yi musu alkawarin yin amfani da kuɗaɗen da aka ba su ta hanyoyin da suka dace.
