
Daga RABI’U SANUSI
Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta ce ta dakatar da Sakataren gwamnatin jihar, Dakta Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggwal daga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar na Kano, Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa ya bayyana hakan cikin wani saƙon murya da aka aika wa Dala FM Kano, a ranar Litinin.
Hashim Dungurawa, ya ce dakatar da ƙusoshin gwamnatin jihar su biyu ya biyo bayan zargin keta alfarmar jagoranci, da ta jam’iyya da kuma keta alfarmar gwamnati, don haka ne suka ɗauki matakin a lokacin da ya dace.
“Jagorancin shugabancin jam’iyyarmu na ƙananan hukumomin da mutane biyun suka fito ya gabatar mana da ƙorafe-ƙorafe kan ƙusoshin gwamnatin akan zarge-zarge da ake musu ya sa muka ɗauki matakin dakatar da su, har sai mun gama bincike”, inji Dungurawa.
Ya ƙara da cewa, dakatar da Abdullahi Baffa Bichi da Muhammad Diggwal ta fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Oktoban 2024 kamar yadda jam’iyyar ta samu ingantattun shawarwari akan zargin da ake musu.
A wani ɓangare, Sakataren gwamnatin, ya barranta kansa da wata kungiyar magoya baya dake ikirarin yana da hannu wajen batutuwa dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani da ake kira da ”Abba Tsaya da Ƙafarka’.
Baffa Bichi ya ce babu wata ƙungiya da ya ke da hannu ciki makamanciyar hakan, don haka ba shi da wata alaƙa da ita.
”Mu na yi wa gwamna biyayya matuƙa da jagoranmu na ɗariƙar Kwankwasiyya ta duniya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso bisa haka, ni ba ni da wata masaniyya kan wancan batun wata ƙungiya da ake alakanta ta da ni.”
A nasa jawabin, ɗan takarar NNPP na kujerar ƙaramar hukumar Bichi, Hon. Hamza Sule Mai Fata, ya ce tsakanin su da Baffa Bichi babu wata matsala.
Hamza Mai Fata ya bayyana haka ne yayin kammala wani zaman sirri da ya gudana da gwamna Abba Kabir da Sakataren Gwamnatin da Kakakin Majalisar Dokokin Kano har ma da sauran masu-ruwa-da-tsaki.
”Mu masu biyayya ne ga Jam’iyyarmu ta NNPP da tafiyar Kwankwasiyya don haka daga yau bazan ƙara rike wannan a matsayin wani abu daban ba.”
”Gaskiya mun godewa mai girma gwamnan mu bisa jajircewarsa wajen haɗa kan magoya bayan mu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa wannan wuta dai na da alaƙa da hana ɗan takarar shugaban ƙaramar hukuma da ya fito daga tsaginsa wanda shi yasa wutar ta ƙara ruruwa.
Saidai, ana ganin irin hakan zata ƙara ruruwa idan har ba’a ɗauki matakin gaggawa ba wanda lallai wankin hula zai iya kawo tsalen badake a jam’iyyar.
Haka kuma a wata majiyar, an ce NNPP ta dakatar na kwamiahinan Sufuri na jihar Kano Hon Muhammad Digwwal bisa dalilin rashin kame baki daga sakin magana da rashin nuna biyayya ga uwar jam’iyya ta jihar.
Kawo yanzu dai, dukkan kallo ya koma sama sakamakon dakatar da manyan Fulogan da ake kallon karansu ya kai tsaiko a wannan Jam’iyya da shugabancinta ya samu damar dakatar dasu a tafiya, yayin da babbar Jam’iyyar adawa watau APC take zawarcin mafi yawancin su.
