Kyautata zaton da al’umma ke yi min ya sa na fito takara a PRP – Hon. Ibrahim Garba

BABANGIDA S GORA a Kano

Ɗan takarar kujerar majalisar tarayya a ƙaramar hukumar Birni dake Jihar Kano ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar PRP, Hon. Ibrahim Garba, ya ce babu abinda ya ja hankalinsa kamar yadda jama’a suke kiraye-kiraye gare shi da ya tsaya ma su takara don ceto al’ummar daga hannun ‘yan sari.

Hon. Ibrahim Garba ya bayyana haka ne a wata zantawa da manema labarai a Kano makonni biyu da suka gabata yayin da yake ma magoya bayan sa babban albishir na irin ƙudurinsa idan ya samu dama a zaɓen 2023 mai ƙaratowa.

Ibrahim ya qara danganta alaƙar Jam’iyyar PRP da irin asalin da take da shi na wanda ya kawo ta Jihar Kano tun asali wato Marigayi Malam Aminu Kano da irin ayyukan a zo a gani na aƙida da ya yi da ya bayyana a matsayin abu mai kyau da ya kamata a yi koyi da shi.

Sannan ya yi batu kan mene ne abinda ya sa idan jama’a sun je karatu ƙasashen ƙetare sun dawo ba a ba su damar tsayawa takara don baje ta su basirar da suke da ita ko da za a iya dacewa daga waɗanda suke kan mulki.

Hon. Ibrahim Ahmad ya ƙara da nuna matuƙar damuwar sa bisa yadda gwamnati ba ta nuna damuwar ta ga al’ummar da take mulka tare da ɗaukar matakin da ya dace wajen yi masu ayyukan azo agani na cigaba.

Don haka ya ce su a yanzu ba su yi wa jama’a alƙawari kamar yadda sauran ‘yan takarkari su ka saba yi, amma kuma babu shakka lokaci ne zai alƙalancin wannan ƙudiri nasu yayin da su ka samu nasara a zaɓe mai zuwa idan Allah ya kai mu.

Da ya juya ɓangaren ɗan takarar shugaban ƙasa kuma Manjo Hamza Al’mustapha, Garba ya ce lallai ayanzu babu wanda ya dace da ƙasar nan kamar sa, kasancewar sa masanim tsaro tun tsawon lokaci.

Sannan yayi misali da yanayin yadda Al’mustapha yabada tsaro da tsayawa ka’in da na’in lokacin tsohon shugaban ƙasa Marigayi Sani Abacha Kuma ya jajirce kan magance matsalolin da suka dami wannan ƙasa.

Haka zalika ya kuma nuna damuwar sa wajen taɓarɓarewar hanyoyi, karatu, rashin samun wadatacce wutar lantarki da Kuma matsalolin tsaro da ƙasar ke fama dashi da yaƙi ci yaki cinyewa.

Ga kuma matsalolin rashin asibitoci da kayan aiki acikin asibitocin da yake barazanar lakume rayuka lokacin da ba’a zato,dan haka yazama dole su yi duk mai yuwuwa dan tsamo al’ummar jihar kano dama ƙasa baki daya daga
Doguwar sumar da tayi.

Daga ƙarshe yayi kira ga jama’a da su yi karatun tanatsu wajen gudanar da zabe da kuma wanda yakamata su zaɓa maimakon zaben tumin dare da zai sa ayi “da na sa ni” daga baya.