Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI
Ci gaba daga makon jiya
Istimna’i kalma ce ta Larabci. A Hausa akan kira mummunar ɗabi’ar da zinar hannu ko auren hannu. A ɗan binciken da na yi, na fuskanci akwai ƙarancin bayanai da ke nuna illolin zinar hannu ga lafiyar jikin mutum.
Hakan ba zai rasa nasaba da rashin bincikenmu ba, mu baƙaƙe da kuma munafincin masu jajayen kunnuwa, saboda su na da wata manufa da suke muradin cimmawa. Kaɗan daga ciki su ne suna so su halasta auren jinsi.
Sannan su na so kasuwar hada-hadar kayan istimna’i ta haɓayyafa. A wannan kasuwa ana siyar da sandararren zakarin roba irin na namiji, ana siyar da wanda mace za ta iya sarrafawa da hannunta sannan kuma ana siyar da mai aiki da kansa.
Abin tsoron shi ne sun ƙirƙiri sandarren gunkin roba na namji da na mace, wanda mutum zai iya siya ya tafi da shi gida. Duk lokacin da ya yi sha’awa ko ta yi sha’awa sai kawai su sadu da wannan gunkin roba. Tab! Wato akwai ƙura!
Su na ta cewa, yin auren hannu ba shi da matsala, wai ya na taimaka wa ɗan adam sanin zurfi da faɗin sha’awarsa. Sai dai kuma hakan ya ci karo da ƙorafin da al’umma ke yi akan illoli da matsaloli da suka fuskanta a sakamakon aikata wannan aiki a zahiri.
Ku biyo ni domin jin irin waɗannan matsaloli da zan kalla na yi bayaninsu a mahangar kimiyyar lafiya a rubutu na gaba da yardar Sarkin halitta.
Naku, MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI
©MIAbdullahi 2024