Legas: Kotu ta tura wani mutum zuwa gidan yari bayan lalata ‘yar shekara 15

Daga BELLO A. BABAJI

Wata Kotun laifukan da suka shafi cin zarafi a Jihar Legas, ta tasa keyar wani mutum mai suna Erickson Iyanagbe zuwa gidan gyaran hali bisa zargin sa da aikata laifin yin lalata da wata ‘yar shekara 15.

Gwamnatin jihar ce ta gurfanar da mutumin bisa laifin saba wa dokar laifukan da suka shafi yin jima’i ta haramtattun hanyoyi ta jihar, ta 2015.

An ruwaito cewa, a shekerar 2023 ne Erickson ya aikata lalata da yarinyar a wani yanki na rukunin gadaje na Greenville Estate dake Ajah a jihar.

Saidai ya musanta aikata laifin a yayin da ake tsaka da sauraren karar, inda ya gaza gamsar da Kotun da bayyanan nasa.

Daga nan ne Alkalin da ya yi hukunci kan karar, Mai Shari’a A.O. Soladoye ya umarci a kai shi gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a sake sauraren karar.

Leave a Reply