Maiduguri na cikin birane mafiya tsaro a Nijeriya – Janar Christopher Musa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hafsan Hafsoshin Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ce Maiduguri babban birnin jihar Borno na daga cikin wurare mafiya tsaro a Nijeriya a halin yanzu duk da rikicin Boko Haram da birnin ya yi fama da shi a baya.

Janar Musa ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da yake ganawa da shugabannin kafofin yaɗa labarai a Abuja.

Ya ce: “Mutane ne kawai suke ganin kamar babu tsaro a Maiduguri, amma birnin na daga cikin waurare mafiya tsaro a ƙasar yanzu haka”.

Babban hafsan tsaron na Nijeriya ya ce rundunar sojin ƙasar ta yi bakin ƙoƙarinta cikin shekara ɗaya da ta gabata wajen ganin an ƙara dakushe ayyukan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da ISWAP.