Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
A wani yunƙuri na cusawa yara ƙanana da al’umma baki ɗaya ilimi da sha’awar ƙwarewa da rubutun harshen Larabci, yanzu haka cibiyar Ideas And Data Global Academy wacce Dakta Mustapha Shehu ya kafa, ta shirya gasar rubuta kalmomin Larabci daidai, wanda makarantu dama ɗaiɗaikun mutane da suka shiga da sunansu sama da 40 ne suka shiga wannan gasar da aka kira Arabic Spelling Bee wanda cikinsu makarantu 27 suka cancanci shiga gasar fidda gwarzo a cikinsu wanda wani yaro mai suna Abdulrahman Shuaibu ɗan ƙasa da shekara 10 ya samu zama gwarzon gasar wanda ya samu kyautar sama da dubu ɗari biyar da kyautar kujerar Makkah sakamakon zaman sa na ɗaya a wannan gasa da wannan cibiya ta shirya a wannan lokaci kamar yadda shugaba kuma wanda ya kafa wannan cibiya Dakta Mustapha Shehu ya tabbatar a lokacin kammala wannan gasa da ta gudana a birnin Kano a harabar Jami’ar Khairun da ke Kano a makon da ya gabata.
Haka kuma ya bayyana cewa akwai buƙatar jihohin Arewa da ma duk inda Musulmi suke a duniya da su tilastawa ko wajabtawa makarantu su da ɗaliban makarantu firmare sakandare da jam’io’i darasin koyon Larabci a duk wani fanni da mutum zai karanta a makarantun gaba da sakandare, domin yin hakan zai taimaka wajen yaɗuwar Larabci wanda yake shi ne harshen Ma’aikin Allah da shi aka saukar da Alƙurani mai girma kuma shi ne harshen ‘yan aljanna kuma hakan zai taimakawa al’umma fahimtar addini da ɗaukakar addinin Musulunci kamar dai yadda Dakta Mustapha Shehu shugaban cibiyar Ideas and Data Global Academy ya tabbatar da hakan.
Ya kuma yi tsokaci da jan hankalin al’umma kan muhimmancin makarantun allo da kuma yadda suka fi makarantun Islamiyya sanin baƙi wanda ya ce duk da matsalolin da ƙalubale da makarantun allo su ke ciki amma ko ya sani cewa addu’o’in su ne suke riƙe da ƙasar nan kuma yana ganin da za a ce dole sai an rushe ɗaya daga cikin makarantu nan biyu na allo da na boko da sai ya zaɓi a bar na allo a soke na boko saboda muhimmancin Alƙur’ani mai girma da ahalinsa, inda kuma ya shawarci hukumomi a matakan tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi su fifita abinda al’umma suke so a yi musu fiye da buƙatun kansu su shugabannin ƙasar nan.
Shi ma a jawabinsa, shugaban shirye-shiryen wannan gasa kuma shugaban cibiyar na Kano, Malam Salim Wada Usman ya ce wannan gasa ba wannan ne karo na farko ba an fara ta ne a Kwalejin Sa’adatu Rimi tun daga safe har dare inda ɗaruruwan ɗalibai masu tarbiyya da mu’amala da jama’a daidai gwargwadon shkarunsu da matsayinsu, sun shiga wanda kuma bayan fafatawa aka zo wannan mataki har aka fitar da wannan gwarzo ciki gwaraza tara cikin wannan mataki wanda kuma akwai wani tsarin na sauran Kano ta Kudu da kuma ta Arewa wanda wannan shi ne kano ta tsakiya kuma su ma za a fito gwaraza tara tara daga shiyoyin domin a haɗasu da waɗannan su kuma a fitar da waɗanda za su fafata a wannan gasa da Ideas and Data Global Academy ta ke shiryawa Dakta Mustapha Shehu
A ƙarshe an miƙa lambobin yabo da kyaututukan kayan abinci da sauran su ga waɗanda suka yi nasara a gasar da ma sauran wasu da suka shiga ko da basu kai matakin nasara ta kusa da ƙarshen ba a kuma karrama wasu mutane da suke hidima ta fanonin da dama wajen ganin wannan gasa ta samu nasara a kowanne matakin da ake yin ta wa Malama Zahrau Garba Ayuba mahaifiyyar Abdulrahman Shuaibu gwarzon a wanan gasa ta bayyana farin ciki wannan nasarar da ta ce addu’a ce da kuma ƙoƙari ya bada wannan nasara inda ta shawarci iyaye su kula da ilimin ‘ya’yansu domin samu nasara da kyakkyawar makoma duniya da lahira.