Malam Shekarau: Baya ba zani

Daga LARABI LARABEEN

Ni ba ɗan siyasa ba ne, amma akwai mutanen da ‘yan siyasa suke raina wa hankali. Suke wasa da ƙwaƙwalensu. Malam Ibrahim Shekarau na ɗaya daga cikin irin waɗannan mutanen duk da kusan duk ‘yan siyasar haka suke. Amma nasa rainin da wasa da ƙwaƙwalwar mabiyansa tana yin yawa.

Sanda Malam Ibrahim Shekarau ya bar Jam’iyyar PDP a 2019 ya koma APC, waɗanne muƙamai Ganduje ya bawa mabiyansa? Hatta Malam Salihu Sagir Takai da yake ɗan a mutum Shekarau, bai iya bamar masa ko da Mai ba Gwamna Shawara ba a mulkin Ganduje na APC.

Sai Takai ɗin ne ya gaji da ga-ludaya ya kai kansa Wajen Ganduje ya samu matsayin Daliget a wannan kakar zaɓen da aka gudanar na zaɓen fidda gwani a APC a 2022.

A yanzu da Shekarau ya yi bankwana da jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso ya koma wajen Atiku. Ya kamata ya faɗa wa magoya bayansa da al’ummar jihar Kano gskyar magana cewar; zai koma wajen Atiku ne saboda kuɗin da aka yi masa tayi da kuma muƙamin da aka yi masa tayi shi kaɗai na Minista idan an kafa gwamnati. Ba zai iya kau da kai a kansu ba.

Idan Shekarau ya ce an masa rashin adalci na rashin bawa yaransa muƙamai a Jam’iyyar NNPP, yanzu da zai koma PDP cire ‘yan takarar PDP za a yi a bawa yaran nasa, su kuma ‘yan PDP din su haƙura?

Ya Kamata idan mutum ya girma ya san ya girma. Duk abinda zai yi ya dinga faɗar gaskiya cikin lamuransa. Ko Shekarau ya koma PDP yaransa ba za su samu muƙami a PDP ba na siyasa. Sai dai na muƙamai da alƙawurra idan an ci zaɓe.

Daga ƙarshe nake cewa ba na siyasa ni ba ɗan siyasa ba ne. Marubuci ne na littattafan soyayya. Tare kuma da sharhi kan al’amuran yau da kullum.

Ana wallafa wasu rubuce-rubucen nawa na ra’ayi da sharhi kan al’amuran yau da kullum a Jaridar Leadership Hausa, da Blueprint Manhaja da Sauran Wasu jaridun da suke amfani da harshen Hausa irinsu Matsefi Daily News da sauransu da dama.

Larabi Larabeen marubuci ne, kuma ɗan ƙasa mai bayyana ra’ayi.