Man City ta kafa tarihin lashe kofuna uku a kaka guda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bayan nasarar Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City wajen lashe kofin zakarun Turai inda ta doke Inter Milan da ƙwallo 1 mai ban haushi, ƙungiyar ta goge guda cikin tarihin da takwararta Manchester United ke tunkaho da shi wato lashe kofunan mabanbantan gasa har guda 3 a kaka guda.

Guardiola ya lashe kofin FA bayan doke Manchester United kana ya yi ƙasa da Arsenal wajen lashe Firimiyar Ingila daga bisani kuma ya je Istanbul ya doke Inter Milan a wasan ƙarshen na zakarun Turai, nasarar lashe waɗannan kofuna 3 ta ba shi damar yin kankankan da zakakurin Manajan Manchester United wato Sir Alex Ferguson wanda ke matsayin manaja ɗaya tilo a Ingila da ya taɓa haɗa wannan kofuna a kakar wasa ta 1998 zuwa 1999.

Yanzu haka dai ƙungiyoyin nan biyu na birnin Manchester wato City da United su kaɗai ke da tarihin lashe kofunan 3 a kaka guda, ko da ya ke a kaf nahiyar Turai akwai ƙungiyoyi irinsu Celtic da Ajax waɗanda su ne na farko da suka kafa wannan tarihi Celtic a kakar wasa ta 1966 zuwa 1967 sai Ajax a kakar wasa ta 1971 zuwa 1972.

Sauran ƙungiyoyin da suka tava nasarar lashe kofunan 3 a Turai sun ƙunshi PSV Eindhoven da Manchester United kana Barcelona sai Inter Milan da kuma Bayern Munich ta Jamus.

Masu sharhi kan harkokin wasannin suka ce Manchester City ba ta iya samun damar kai wa ga wannan nasara ta lashe kofin zakarun Turai karon farko a tarihi ba, bayan yunƙurin lashe kofin sau 13 ciki har da kai wa wasan ƙarshe amma Chelsea ta maketa sai da ta karya dokoki 115 wanda yanzu haka ta ke fuskantar tuhuma akai.

Nasarar dai ta zamo babban dako da Manchester City ta shafe tsawon lokaci ta na yi tun bayan saka ƙafarta karon farko a gasar cikin kakar wasa ta 1969, kuma daga kakar wasa ta 2012 zuwa yanzu an ga yadda ƙungiyar ta kai wasannin gab da na kusa da ƙarshe sau 3 sai wasan gab da ƙarshe sau 2 kana wasan ƙarshe shima sau biyu gabanin samun nasarar.

Mutane da dama na kallon zuwan Haaland Manchester City a matsayin wata gagarumar gudunmawa da ta kai ƙungiyar ga nasarar lashe wannan kofi na gasar zakarun Turai da ta shafe tsawon lokaci ta na nema da kuma zuba maƙuden kuɗaɗe, masu sharhi kan wasanni na Turai na ganin gudunmawar ta Haaland ba wata abar azo a gani ba ce idan an kwatanta da sadaukarwar wasu tarin ’yan wasa a tafiyar ciki kuwa har da Kevin de Bruyne da Ilkay Gundogan baya ga Jack Grealish dama Bernado Silva.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *