Maryam Yahaya ƙanwata ce ba soyayya muke ba – Jarumi Shamsu Ɗan’iya

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Fitaccen jarumi a masana’atar Kannywood, wato Shamsu Ɗan’iya ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa dangane da cewa wai zai auri Maryam Yahaya.

A yan kwanakin nan kafafen sada zumumta na Social Media da wasu Jaridun ƙasar nan sun ta yayata cewa Shamsu Ɗan’iya zai angoce da Jaruma Maryam Yahaya.

Shamsu Ɗan’iya da a yanzu aka fi kira da Hisham, ya ce daga lokacin da aka fara yaɗa jita-jitar zuwa yanzu a kodayaushe yana karva kira daga wajen mutane daban-dadan.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Blueprint Manhaja, Ɗan’iya ya ce abin ya samo asali ne tun lokacin da suka yi tafiya zuwa Ƙasar Dubai yayin ɗaukar shirin fim ɗin ‘Alaka’ an gansu a hotuna da dama a can.

Kazalika ya cigaba da cewa, “mafi yawa idan muka je taruka haka akwai masu bibiyar mu da masu ɗaukar hoto da ‘yan jarida ana ɗaukar hoto ana yaɗawa. Ita kuma duk lokacin da muka haɗu za ka ga cewa akwai abin da muke tattaunawa, to a daidai lokacin da muke tattaunawa ne za ka ga an ɗauke hotuna sai ai ta yaɗawa. To shi ya sa mutane suke alaqanta abin da cewa muna soyayya ko abinda ya yi kama da haka. Amma babu wannan maganar, Maryam Yahaya ƙanwata ce, muna mutunci da ita.”

In dai ba a manta ba ko a ‘yan watanni baya an dinga yayata cewa, Shamsu Ɗan’iya zai auri ‘yar maigidansa Ali Nuhu, wato Fatima Ali Nuhu, wanda shi ma ya musanta.

Wannan dai ba sabon abu ba ne wajen yaɗa jita-jita irin wannan, musamman ma a masana’atar fim ta Kannywood.