Zaɓen 2023: Ku tanadi abinci na kwana 3, kiran Amurka ga ‘ya’yanta mazauna Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya shawarci Amurkawa mazauna ƙasar da su tanadi abinci da ruwa da sauran kayan buƙatu na kwana uku don samun abin da za su ci ko da ta kasance an hana zirga-zirga yayin zaɓubɓukan da ke tafe.

Kazalika, ofishin ya gargaɗe su kan yiwuwar samun zanga-zanga da kuma taƙaita zirga-zirga a lokutan zaɓuɓɓukan.

Don haka ya ja hankalin Amurkawa mazauna Nijeriya da su guji shiga tarurruka saboda suna iya rikiɗewa su zama rikici.

Ofishin ya yi wannan gargaɗin ne a shafinsa na intanet a ranar Litinin.

Inda ya ce, “Gwamnatin Nijeriya za ta hana zirga-zirgar abubuwan hawa a faɗin ƙasar a lokacin zaɓe.

“Bayanai daga Gwamnatin Nijeriya sun nuna jami’an tsaro da na INEC da masu sanya idon da aka tantance kaɗai za a bai wa damar zirga-zirga.

“Lura da yadda zaɓubbukan baya suka gudana, muna sa ran hanyoi za su kasance a rufe daga ƙarfe 00:00 zuwa 18:00 a ranar 25 ga Fabrairu da kuma 00:00 zuwa 18:00 ran 11 ga Maris.

“Ku sani cewa ana iya tsawaita hana zirga-zirga zuwa kowane lokaci. Don haka ku zama masu bibiyar bayanan Gwamnatin game da taƙaita zirga-zirgar.”