Tsohon ɗan wasan shirin BBNaija ya bayyana kwaɗayinsa na son ɗarewa kujerar maigabatar da shirin

Daga AISHA ASAS

Sanannen tsohon ɗan wasa a shahararren shirin nan mai farin jini na Big Brother Naija, Adekunle Olopade, ya bayyana kwaɗayin sa na zama magajin mai gabatar da shirin, wato Ebuka Obi Uchendu, idan buƙatar sauya shi ta taso a nan gaba.

Adekunle ya yi wannan roƙo ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Matashin mai kimanin shekaru ashirin da bakwai a duniya, ya yi amfani da kafar sada zumunta ta Twitter ne don aika ƙoƙon barar nasa ga waɗanda abin ya shafa, ta hanyar yaɗa saƙon nasa a ainahin shafin shirin na gabaɗaya, wato Big Brother Africa. Ya yi hakan ne don tabbatarwa shuwagabannin wannan shiri da gaske yake, ba zancen wasa ba.

A cikin jawabin nasa, Adekunle Olopade ya sheda masu cewa, yanzu ne ya fi dacewa su yi wannan hukunci na yiwar ba shi wannan dama, ta hanyar janyo shi a aikin don ya koya daga maigabatarwa na yanzu, wato Ebuka.

“Yanzu ne ya dace in fara sanin kan zaren, ta hanyar koya daga Ebuka. A shirye nake tsaf don saka duk ƙarfina wurin ganin na koyi aikin, kuma Ina fatan zama maigabatarwa na shirin Big Brother Naija wata rana. Ina ganin abu ne da zan iya yi,” inji Adekunle Olopade.