Apama ya karya azumin sa kan zancen fasfon Amurka da ya mallaka

Daga AISHA ASAS

Shahararren ɗan wasan barkwanci Dike Osinachi, wanda aka fi sani da Apama Egbeigwe ya magantu kan yadda mutane suka juya bidiyon da ya sake kan sha’anin mallakar fasfon Ƙasar Amurka da ya yi, bayan tsayin lokaci da ya ɗauka bai tanka ‘yan gutsiri-tsoma kan zancen.

A makwanin baya ne Apama ya wallafa wani faifan bidiyo, inda ya nuna cikin alfahari cewa, ya mallaki shedar izinin zama ɗan ƙasa na Amurka, ta hanyar nuna fasfon Ƙasar Amurka da ya ce ya mallaka tare da na gida Nijeriya. Wanda ya nuna cewa, yanzu shi mazauni Ƙasar Amurka ne kamar yadda yake mazaunin Nijeriya.

Wannan bidiyo dai ya samu martani da dama daga mabiyan wannan jarumi, sai dai kaso mai yawa ba abu mai taya murna suke faɗa ba. Kamar yadda jarumin ya faɗa, da yawa cikin masu biyo bahasin zancen ta hanyar kiran wayarsa, ko turo masa da saƙo da kaso mafi yawa na masu martani a ƙarƙashin bidiyon suna tambayar yadda ya mallaki wannan damar ta zama mazauni a babbar ƙasa irin Amurka. Yayin da wasu ke neman ƙarin bayyanin yadda ya samu don su ma su bi matakan don su mallaka.

Apama ya karya azumin shiru na ƙin amsa tambayoyin masu tambayar ta sa da cewa, gaskiyar fasfon da ya nuna dai ba nasa ba ne, na wani ne ya yi amfani da shi, don raha. Kuma ya ƙara da abinda ya fahimta a wannan bidiyo da ya saki, inda yake cewa, ya fahimci muhimmancin mallakar fasfon Ƙasar Amurka ga ɗan Nijeriya, wanda da a ce da gaske ne ya mallaki fasfon ɗin zai zama wani allon talla ga ‘yan Nijeriya, watakila ma a kafa wani allo don girmamawa gare shi.

Daga ƙarshe ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zama masu alfahari da ƙasarsu, kuma ‘yan ƙasa na ƙwarai ta hanyar zaɓen shuwagabanni da suka da ce a zaɓe mai zuwa, don ƙasarmu ta zama abin sha’awa ga wasu ƙasashe, har da Ƙasar Amurkan da muka kwaɗaita da ita.