Zaɓen 2023: Kano ta zarce ko’ina yawan ejent da mutum 145,393

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar da adadin wakilan jam’iyyu a rumfunar zaɓe da wajen tattara sakamako kamar yadda jam’iyyu suka miƙa wa INEC sunayensu.

Kamar yadda bayanan INEC suka nuna, ejent 1,574,301 ne za su wakilci jam’iyyu a baki ɗaya rumfunan zaɓe, sannan ejent 68,057 a wajen tattara sakamako a faɗin ƙasa a yayin zaɓe mai zuwa.

Bisa wannan lissafi, ejent 176,223 ne za su wakilci Jam’iyyar APC mai mulki, Jam’iyyar PDP kuwa na da 176,558, yayin da NNPP ke da wakilai 176,200 a faɗin ƙasa.

Idan aka haɗe wakilan na jam’iyyu ukun da ke kan gaba, wato APC da PDD da kuma NNPP, Jihar Kano APC ce ke da wakilai mafi yawa inda take da mutum 145,393, sai Legas da ke bi mata da mutum 98,646, sai kuma Jihar Ribas da ke da 79,795.

Gaba sai Jam’iyyar Labour (134,874 PUAs da 4,859 CAs); Accord (83,007 PUAs da 3,358 CAs); Action Alliance (56,459 PUAs da 1,531 CAs); African Action Congress (38,779 PUAs da 1,723 CAs); African Democratic Congress (96,043 PUAs da 3,626 CAs).
Action Democratic Party (44,516 PUAs da 548 CAs); All Progressives Grand Alliance (25,657 PUAs da 933 CAs); Allied Peoples Movement (80,892 PUAs da 3,932 CAs); Action Peoples Party (64, 798 PUAs da 2,546 CAs); Boot Party (13,544 PUA da 620 CA).

National Rescue Movement (87,014 PUAs da 3,805 CAs); Peoples Redemption Party (87,562 PUAs da 3,452 CAs); Social Democratic Party (98,313 PUAs da 3,310 CAs); Young Progressive Party (76,199 PUAs da 3,151 CAs) da kuma Zenith Labour Party (57,563 PUAs da 1,939 CAs).