PSC ta cire Naja’atu daga aikin zaɓe

Daga WAKILINMU

Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanda ta Ƙasa (PSC), ta cire sunan Hajiya Naja’atu Mohammed, daga jerin waɗanda za su yi aikin sanya ido kan ayyukan ’yan sanda yayin zaɓe mai ƙaratowa.

Wannan na zuwa ne bayan da Jam’iyyar APC ta soki sanya sunanta daga jami’an da za su aiki tare da ’yan sanda yayin zaɓubɓukan.

Bayan da hukumar PCS ta bayyana sunan Naja’atu ba da jimawa ba mai magana da yawun Jam’iyyar APC, Festus Keyamo, ya fitar da sanarwa a ranar Litinin inda suka buƙaci a gaggauta janye sunan Naja’atu.

Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun Keyamo, APC ta ce ko kaɗan naɗin Naja’atu bai dace ba, tana mai cewa hakan takala ce a zahiri, lamarin da a cewarta Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Shettima ba zai yarda da shi ba.

Ba tare da ɓata lokaci ba hukumar ta janye naɗin na Naja’atu biyo bayan caccakar da ta sha daga APC da wasu ɓangarori.

Hukumar ta ce kafin yin naɗin sai da ta tuntuɓi tsohon Mataimakin Sufeto-Janara na ’Yan Sanda, Bawa Lawal (mai murabus) wanda ya fito daga shiyya guda tare da Najatu don ta gaje shi wajen aikin sanya ido kan ayyukan ‘yan sanda a yankin yayin zaɓe.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, “Hukumar za ta ci gaba da kasancewa mai sauraron muradin ’yan Nijeriya da kuma ba da gudunmawarta ga cigaba da kuma ɗorewar dimokuraɗiyyar ƙasar.”

Ani ya ba da tabbacin hukumar za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da zaɓe mai tsafta a 2023 ta hanyar sauke nauyin da ya rataya a kanta.