Masanan Afirka sun bayyana ra’ayoyinsu kan tasirin da taron wakilan JKS karo na 20 Zai haifarwa Sin da duniya

Daga CMG HAUSA

A cikin kwanakin da suka gabata a jere, taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Sin karo na 20 ya janyo hankalin ƙasa da ƙasa matuƙa.

Yayin da aka rufe taron, masanan Afirka sun bayyana cewa, taron yana da babbar ma’ana, wanda zai haifar da babban tasiri ga kasar Sin, har ma zai ƙara kuzari ga ƙasashen duniya wajen yin haɗin gwiwa don tinkarar ƙalubale da samun bunƙasuwa tare.

Darektan cibiyar nazarin harkokin Sin dake Nijeriya Charles Onunaiju ya yi nuni da cewa, Sin tana son samar da gudummawa ga sauran ƙasashen duniya wajen samun ci gaba, kana bunƙasuwar ƙasar Sin za ta yi tasiri ga duniya baki ɗaya.

Don haka, yana fatan ƙasashen duniya za su koyi fasahohi da shirye-shiryen samun ci gaba na ƙasar Sin da kuma damar haɗin gwiwa daga taron wakilan JKS karo na 20, ta yadda za a tafiyar da harkokin duniya da ma tinkarar ƙalubalen da duniya ke fuskanta tare.

Farfesa Costantinos Berhufesfa na jami’ar Addis Ababa ta ƙasar Habasha ya yi nuni da cewa, nasarorin da ƙasar Sin ta cimma a aikin zamanintar da kanta bisa tsarinta, sun ƙarfafa gwiwar ƙasashen duniya musamman ma ƙasashe masu tasowa, wannan zai baiwa sauran ƙasashe masu tasowa damar zabar dabarun raya ƙasashesu dake dacewa da yanayinsu.

Mai fassara: Zainab