Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin sakin Nnamdi Kanu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Biyo bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wacce ta saki jagoran ƙungiyar ’yan ta’addan Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli.

A ɗaukaka ƙarar da aka shigar a ranar 19 ga Oktoba, 2022, a gaban Kotun Ƙoli ta ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Gwamnatin Tarayya ta buƙaci Kotun Ƙoli ta dakatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a ranar 13 ga Oktoba, 2022, wanda ya saki shugaban na ƙungiyar ‘yan awaren Biyafara.

Gwamnatin Tarayya a cikin shaɗarar ɗaukaka ƙara ta bakwai, ta yi Allah-wadai da matakin da ƙaramar kotun ta yanke, sannan kuma ta buƙaci a yi watsi da shi.

Gwamnatin Tarayya ta yi iƙirarin cewa, kotun ɗaukaka qara ta yi kuskure a lokacin da aka dawo da Kanu, domin fuskantar shari’a bayan ya tsallake beli ya gudu daga ƙasar.

Ta kuma yi iƙirarin cewa, Kotun Ɗaukaka Ƙarae ta yi kuskure lokacin da ta soke tuhumar da ake yi wa Kanu bisa hujjar cewa, kotun da ke shari’ar ba ta da hurumin cigaba da shari’ar, saboda yadda aka mayar da Kanu ƙasar bisa zargin tsalleke beli.
Yanzu ana dakon ranar da za a saurari ƙarar a nan gaba.