Abinda ya sa Buhari tsige Shugaban Hukumar Neja-Delta

*Majalisar Dattawa ta gayyaci Ministan Neja-Delta bisa zargin almundahanar Naira Biliyan 480
*An danganta tsige Shugaban NNDC da Ministan

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A jiya Alhamis ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tsige Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (wato NDDC), Mista Effiong Akwa.

Sanarwar da ta fito daga hannun mai magana da yawun Ma’aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta, Patricia Deworitshe, ta ce, tsige Akwa da Buhari ya yi ya soma aiki ne daga jiya, 20 ga Oktoba, 2022.

Sanarwar ta qara da cewa, a baya an naɗa Mista Akwa shugaban NDDC ne na wucingadi tsawon wa’adin lokacin da za a kammala binciken harkokin hukumar, don haka kammala binciken na nuna riƙon da aka bai wa Akwa ya zo ƙarshe kenan.

A cewar sanarwar, “Shugaba Buhari ya amince da kafa sabon kwamitin gudanarwa na hukumar daidai da tanadin Sashe na 5(2) na dokar da ta kata Hukumar NDDC ta 2000.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “za a tantance sunayen waɗanda aka zaɓa na sabuwar tawagar gudanarwa da hukumar gudanarwa, inda za a miƙa su ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa, don amincewa.”

Ma’aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta ce mai haƙƙin kula da hukumar ta NDDC.

Sai dai ba a yi wani ƙarin haske da kan dalilin Shugaba Buharin na korar Effiong Akwa daga muƙamin nasa ba baya ga ƙarewar wa’adin binciken.

To, amma a wani ɓangaren kuwa, Majalisar Dattawa, ta hannun kwamitinta mai kula da ɗa’a da ƙorafe-ƙorafen jama’a, ta gayyaci Ministan Harkokin Neja Delta, Umana Okon Umana, bisa zarge-zargen almundahanar Naira biliyan 480 da kuma cin hanci da rashawa.

Shugaban kwamitin, Sanata Ayo Akinyelure, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, ya ce, ƙarar da kwamitin ya shigar a gaban majalisar ya yi zargin cewa, ministar na taimaka wa ayyukan cin hanci da rashawa kuma ta kasa ƙaddamar da hukumar gudaarwar raya yankin Neja Delta (NDDC).

A cewarsa, an kuma zargi ministan da ƙoƙarin tunkuɗe gurbin shugaban hukumar ta NDDC, wato Effiong Akwa, wanda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi bisa ƙa’ida, kuma Majalisar Dokoki ta ƙasa ta tabbatar da shi tare da korar ma’aikatan NDDC sama da 700.

Sanatan ya kuma yi iƙirarin cewa, Umana ya kammala shirye-shiryen neman amincewar Shugaban Ƙasa, domin karɓar waɗannan kuɗaɗe da sunan cewa za a kashe a wasu ayyuka na musamman a yankin Neja Delta.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a harabar Majalisar Dokokin Ƙasa da ke Abuja, Sanata Akinyelure ya ce, “akwai kuɗi Naira Biliyan 480 a asusun CBN.

“An ce, Umana Umana ya kammala hanyoyin da zai gabatar da wasu sabbin ayyuka ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin ya amince masa ya fara amfani da kuɗin wajen aiwatar da ayyukan da majalisar ƙasa ba ta yarje ba.

Sanata Akinyelure ya ce, wasu zarge-zarge da dama da ake yi wa Umana; daga ciki har da ƙin miƙa kasafin kuɗi na shekara biyu na NDDC (2021 da 2022) ga Majalisar Dokoki ta ƙasa domin amincewa da kuɗaɗen da hukumar ke kashewa bisa umarnin ministar don haka ya ɗauki ikon kasafta wa kansa.

Haka zalika, an kuma zargi ministan da yunƙurin ƙorar shugaban hukumar ta NDDC mai ci a yanzu, Effiong Akwa wanda shugaba Buhari ya nzda tare da maye gurbinsa da ɗaya daga cikin muƙarrabansa.

Ƙoƙarin da ke gaban majalisar dattawan ya kuma zargi Umana da ƙin ƙaddamar da hukumar ta NDDC da gangan.

Don haka Sanata Akinyelure ya bayyana cewa, an gayyaci ministar da ta bayyana gaban kwamitin a ranar 10 ga watan Nuwamba domin bayar da amsa ga dukkan zarge-zargen.
Tuni dai wasu masu hasashe sun fara danganta tunɓuke Akwa da haɗin bakin Umana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *