Nijeriya na da kyakkyawar makoma a hannunmu – Buhari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, duk da ƙalubalan tattalin arziki da duniya ke fuskanta da faɗuwar farashin mai wanda hakan ya haifar wa ƙasa ƙarancin kuɗin shiga, gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin ɗora Nijeriya kan turbar cigaba.

Buhari ya ce duba da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu ƙarƙashin Jam’iyyar APC, jami’yyar na da dukkan dalilan da za su ta yin alfahari da hakan.

Shugaban ya bayyana haka ne a Juma’ar da ta gabata, sa’ilin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe Shugaban Ƙasa (PCC) da sauran tsare-tsaren yaƙin neman zeɓe na ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Buhari ya yi alƙawarin zai kasance kan gaba wajen zaɓen tsohon gwamnan Jihar Legas a matsayin wanda zai gaje shi a 2023.

Ya ce, zaɓen Tinubu a matsayin magajinsa zai taimaka wajen ɗorawa daga inda zai tsaya don ci gaba da yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata.