Dubai ta dakatar da bai wa ‘yan Nijeriya biza

Daga BASHIR ISAH

Hukumomin Dubai sun ba da sanarwar dakatar da bai wa ‘ya Nijeriya biza ta shiga ƙasar har sai abin da Allah Ya yi.

Bayanin dakatawar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da suka aika wa abokan kasuwancinsu na Nijeriya.

Dubai ta ce ta dakatar da dukkan yakardun da aka tura mata don neman biza daga Nijeriya.

Bayanai sun ce wannan mataki da Dubai ta ɗauka na da nasaba da matsayar da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Haɗaɗɗiyar Dular Larabawa ta cimma, tare da cewa dakatarwa ta shafi dukkan ‘yan Nijeriya ne.

Sanarwar ta ƙara da cewa, kuɗaɗen da aka biya da farko don neman bizar sun bi ruwa don kuwa, babu batun maida su.

“Ku sanar da abokan hulɗarku su sake miƙa takardar neman biza bayan magance matsalar da ke tsakanin gwamnatocin biyu (Nijeriya da Dubai),” cewar sanarwar ga kamfanonin jiragen sama a Nijeriya.