APC a Zamfara ta yi Allah wadai da harin da PDP ta kai wa mutane a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara, a cikin kakkausar murya ta yi Allah-wadai da harin da wasu ‘yan bangar siyasa na jam’iyyar suka kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a Gusau babban birnin jihar.

Sakataren yaɗa labaran Jam’iyyar APC na jihar Yusuf Idris ya yi wannan martanin a wani taron manema labarai.

“Dukkanmu muna sane da munanan abubuwan da ke faruwa a jihar mu abar ƙauna, inda a jiya Asabar wasu ‘yan bangar Jam’iyyar PDP suka far wa wasu matasanmu da ba su ji ba ba su gani ba, a lokacin da ɗan takarar gwamna, Dakta Dauda Lawal Dare ya shigo babban birnin jihar Gusau.

“Haka zalika mun damu matuƙa da irin wannan mummunan aika-aika da ‘yan barandan PDP suka yi da suka yi amfani da zuwan ɗan takararsu wajen tada zaune tsaye,” Yusuf ya ce.
Jam’iyyar ta bayyana harin da ake zargin PDP da kai wa mutanen jihar a matsayin na dabbanci.

Jam’iyyar ta zargi Dakta Dauda Lawal Dare da ɗaukar nauyin wasu mutane sanye da kayan soja a cikin ayarinsa da suka zo Gusau suka harbe waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.

“Lokacin da Dakta Dauda ya iso Gusau a ranar Asabar, ‘yan barandan siyasarsa sun harbe ‘mutane uku har lahira da ba su ji ba ba su gani ba, inda muka samu rahoton cewa wasu mutum 20 sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.”

Jam’iyyar ta buƙaci jami’an tsaro a jihar da su bankaɗo manufar harin da ake zargin PDP ta kai tare da tabbatar da kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su gaban kuliya.

“Da umarnin dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar da gwamnatin jihar ta bayar a baya-bayan nan don sake dawowar ayyukan ta’addanci a jihar, ya kamata Jam’iyyar PDP ta mutunta hakan ta hanyar ajiye gwagwarmayar siyasarsu a gefe tare da ganin tsaron jama’a a matsayin mafi muhimmanci.”

Jam’iyyar ta APC, ta yi kira ga ‘ya’yanta da su kwantar da hankalinsu da kuma kasancewa masu bin doka da oda domin a samu zaman lafiya.

A halin da ake ciki, da yake mayar da martani kan zargin APC, mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Alh. Muktar Lugga ya musanta zargin da Jam’iyyar APC ta yi, yana mai bayyana hakan a matsayin mugun nufi da rashin gaskiya.

Lugga ya bayyana cewa PDP ba ta tava kasancewa cikin jam’iyyar da ke goyon bayan duk wani nau’in ‘yan daba ko haddasa tashin hankali a lokacin yaƙin neman zaɓe ko kuma a zaɓe mai zuwa a jihar.

“Mu jam’iyya ce mai bin doka da oda kuma muna mutunta ƙa’idojin doka amma za mu ci gaba da mutunta dokokin jam’iyyarmu da tsarin mulkin tarayyar Nijeriya a duk harkokin siyasarmu a jihar a yaɓin neman zaɓe da sauran su,” Lugga ya ce.