Masari ya ba wa Rarara da Baban Chinedu tallafin N80m

Daga Umar Garba a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina, qarqashin jagorancin Aminu Bello Masari ta bawa fitaccen mawaqin siyasa, Adamu Abdullahi Rarara tallafin kuxi naira miliyan 50.

A yayin da aka bawa xan wasan barkwanci Kuma Mawaqin Hausa, wato Baban Chinedu Naira miliyan 30.

Bayanin hakan dai na qunshe ne a cikin wata takarda mai xauke da sa hannun Saminu Muhammad K. Soli, kwamishinan kasafin kuxi da tsare-tsare na jihar.

Ma’aikatar kasafin kuxin ta ce an amince da sakin Naira miliyan 80 ga mutanen biyu a matsayin taimako kan lalata gidajensu a jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *