Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Ranar 25 ga Yuni ce aka tsayar a matsayin ranar yaƙi da tu’ammalli da miyagun ƙwayoyi ta duniya.
Jihar Kebbi ita ma ba a bar ta a baya ba wajen shiga sahun sauran sassan duniya wajen yekuwar yaƙi da tu’ammalli da miyagunƙwayoyi inda a wani haɗin gwiwa tsakanin ofishin Hajiya Zainab Nasir (Nasare) matar Maigirma gwamnan jihar Malam Nasir Idris da kuma hukumar yaƙi da sha da kuma fataucin miyagunƙwayoyi (NDLEA) reshen jihar ta Kebbi ta gudanar da wani gangamin wayar da kai dangane da illar shaye-shaye tsakanin al’umma musamman matasa a garin Birnin Kebbi ranar Talatar da ta gabata.
Honarabul Yakubu Ahmed Birnin Kebbi kwamishinan yaɗa labarai shi ne ya wakilci uwargidan gwamnan ya bayyana cewa matsalar shaye-shaye matsala ce da addabi matasa duk faɗinƙasar nan saboda haka yana da kyau a ɗauki matakan yaƙi da wannan matsalar da ta addabi matasa musamman marasa aikin yi, idan aka samar da abin yi ga matasa in Sha Allahu za a sami sauƙin ta sosai ko da kuwa ba a magance ta gabaɗaya ba.
Haka-zalika aikin haɗin gwiwa shi ma zai iya bayar da gagarumin gudummawa, musamman tsakanin ofishin matar Maigirma gwamna da wannan hukumar ta yaƙi da tu’ammalli da miyagunƙwayoyi da kuma makarantun firamare, sakandare har zuwa na gaba da Sakandare da kuma masarautun gargajiya da ya ke su ne suka fi kusantar al’umma.
Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar yaɗa labarai da dukkannin rassanta a shirye su ke da su bayar da nasu gudummawa wajen ganin an sami nasara a cikin wannan aikin.
