Na fara aiki a matsayin mai hidimar ƙasa Allah ya maida ni CMD a FMC Azare – Dr Abdullahi

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITAB a Kano

Dr Abdullahi Ibrahim,ƙwararre ne a fannin cututtukan ƙwaƙwalwa da shanyewar ɓarin jiki, farfaɗiya, ciwon kai da sauransu, kuma a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ya bayyana cewa wanda ma’aikaci ne a babban asibitin Gwamnatin Tarayya da ya ke Azare a Jihar Bauchi, wanda kuma tsohon shugaban asibitin ne da ake kira a Federal Medical Center, (FMC) wanda tarihinsa ya nuna cewa ya je wannan asibiti ne a matsayin ɗan bautarƙasa a shekarar 2000 kuma bayan ya zama cikakken ma’aikaci ne a sibitin sai kuma a shekarar 2014 ne ya zama shugaban wannan asibiti har zuwa shekaru 8 inda ya sauka a matsayin CMD a shekarar 2022 wannan ya ce baƙaramar nasara ba ce a rayuwarsa kuma akwai darasi a cikin wannan bayani da ya kamata al’umma musammam matasa su ɗauka daga wannan abu da Allah ya ƙaddara haka.

Haka zalika daga cikin abubuwan da ya ke ganin abin farin ciki ne da godewa Allah na tarihi ciyar da wannan asibiti gaba shi ne akwai lokacin da wannan FMC akwai sashin da ake kira na dindindin na wannan asibiti to a lokacin wurin yana matsayin asibitin sha ka tafi ne ba a kwantar da majinyata amma da taimakon Allah da kuma aiki na waɗanda na gada suka yi tun daga kan Dr Abubakar Dauda Katagum, da sauran shugabanni suka yi a wannan wuri ni ma na zo na ɗora. Akwai gine-gine na ɗakunan bincike da aka gina da sahalewar gwamnatin tarayya ta wannan lokaci sai kuma sashin kula da cututtukan ido wanda muka samu tallafi daga gwamnan bankin Nijeriya, na wancan lokacin Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sunusi II, lokacin yana gwamnan banki CBN ba shakka akwai abubuwa da dama da a zamani na Allah, ya tabbatar da su wannan FMC ina farinciki da godewa Allah, da wannan dama da ya bani yanzu dai ina aiki a wannan wuri a matsayin ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa da sauran cututtuka da na faɗa a baya.”

A ƙarshe Dr Abdullahi Ibrahim, ya shawarci al’umma da ta kula da lafiyarsa da kuma tanadi ta hanyar yin aiki tuƙuro da dogaro da kai ko ta hanyar noma ne kasuwanci ne kuma a riƙa haɗawa da hakuri da addua domin rayuwar tana buƙatar haƙuri da addua da yanayin da aka samu kai na al’amuran rayuwa.

By ukarofi