Matasa sun gudanar da gagarumin taro kan takarar Yahaya Bello a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An gudanar da taron dandazon mata da matasa a Kano na magoya bayan Gwamna Yahaya Bello dake neman ya tsaya takarar shugabacin ƙasa a 2023, saboda cancantarsa da salon iya mulkinsa.

Taron ya gudana ne a ranar Asabar da ta gabata a ƙarƙashin ƙungiyar ‘Rescue Nigeria Mission’ dake yaɗa da’awar takarar gwamnan a faɗin Nijeriya.

A jawabinsa, jagoran ƙungiyar na jihar Kano Abdul Amat Maikwashewa ya bayyana cewa su ne suka roƙi Gwamna Yahaya Bello ya fito takara a 2023 bisa la’akari da cancantarsa a kowane fanni, ga shi matashi mai jini a jika, ya ƙware wajen iya shugabanci sannan uwa uba shi ne shugaban da ya damu da damuwar talaka.

Maikwashewa ya ce gwamnan ya janyo mata da matasa a jikinsa kuma ya dage wajen ganin ya bunƙasa rayuwar matasan Nijeriya, ga shi kuma  ba ya ƙyamar jama’a sannan ya ƙirƙiri kyawawan ƙudurori da manufofi na cigaban jama’a.

A cewar jagoran matasa za su amfana gaya muddin Yahaya Bello ya zama shugaban ƙasar Nijeriya a 2023. Ya ce ko a lokacin zavukan ƙananan hukumomi a jiharsa ta Kogi ya bai wa mata da matasa dama kuma sun ci zaɓuka rututu a jihar.

Shi ma da yake nasa jawabin a wajen taron, Shugaban Ma’aikatan Gwamnan Kogi Abdulkarim Jamiu Asuku ya yaba wa dandazon Kanawa mata da matasan su bisa fitowa ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin nuna goyon bayansu ga Yahaya Bello.

Asuku ya ƙara da cewa lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagorancin ƙasar nan ta hannun Gwamna Yahaya Bello, domin ɗimbin cigaban da zai kawo a ƙasar nan.