Matawalle ya yaba da haɗin kan da Zamfarawa suka bai wa zaɓen gwamnonin

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yaba wa masu kaɗa ƙuri’a da suka fito ƙwai da ƙwarƙwata domin kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun jihohi a jihar.

Gwamnan ya yi wannan yabon ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’a a mazaɓarsa da ke garin Maradun, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Maradun, a wata hira da manema labarai ranar Asabar.

Ya nuna jin daɗinsa da yanayin tsaro a jihar tare da yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, NEC, bisa yadda ta raba kayan zaɓe a kan lokaci a faɗin jihar.

“Na yaba da ƙoƙarin da hukumomin tsaro da kuma hukumar INEC ke yi na tabbatar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da aminci a jihar,” in ji shi.

A cewarsa, APC ce za ta lashe jihar kamar yadda ya yi alƙawarin gudanar da mulkin jihar zuwa wani matakin cigaba idan aka sake zaɓensa a karo na biyu.

“Insha Allahu za mu ci zaɓe, kuma Jihar Zamfara za ta ci gaba ta fannin jin daɗin al’ummar jihar da tattalin arziki ƙarƙashin kulawarmu,” in ji Gwamnan.

Ya shawarci hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen ganin an gudanar da zaɓen cikin lumana a jihar.

Hakazalika, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma zaɓaɓɓen Sanata a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Alh. Abdulaziz Yari, a wata hira da manema labarai jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’a a mazaɓarsa dake Talata Mafara hedikwatar ƙaramar hukumar Talata Mafara, ya bayyana zaɓen gwamnonin na majalisun jihohin da cewa komai na gudana cikin kwanciyar hankali.

Yari ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar da su kasance masu bin doka da oda a koda yaushe, tare da guje wa duk wani abu na haifar da tashin hankali a lokacin zaben da kuma bayansa don ba wa INEC damar gudanar da sahihin zaɓe a jihar .