Mazauna Chikun sun yi zanga-zanga kan harin ta’addanci a yankinsu

Daga BASHIR ISAH

Mazauna yankin Chikun cikin Ƙaramar Hukumar Goningora da ke Jihar Kaduna sun tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a yankinsu sakamakon zanga-zangar da suka gudanar a ranar Alhamis.

Jaridar Intelrigeon ta rawaito cewar, mazauna yankin sun shirya zanga-zangar ne domin nuna rashin jin daɗinsu da harin ta’addancin da ‘yan bindiga suka kai yankin.

Zanga-zangar ta yi sanadiyar hana abubuwan hawa zirga-zirga a hanyar kamar yadda aka saba.

A cewar tashar Channels TV, mazauna yankin da dama ne aka yi awon gaba da su yayin da wasu sun jikkata sakamakon harin ‘yan bindiga a yankin a ranar Laraba.

Tashar ta ƙara da cewa, mutum biyu sun mutu sakamakon harin, lamarin da ya fusata jama’ar yankin wanda ya kai ga sun shirya zanga-zanga.

Harin na zuwa ne kimanin mako guda bayan da sojoji suka kashe gawurtaccen ɗan ta’adda, Boderi Isyaku da wasu mutanesa a yankin.