Teku ta ci matashi a Legas

Daga BASHIR ISAH

Rahotannai daga Jihar Legas sun ce, teku ya yi gaba da wani matashi ɗan shekara 13, mai suna Kelvin Onyengba, a lokacin da suka je shaƙatawa tare da abokansa a bakin teku a yankin Ajah da ke Legas.

Majiyarmu ta ce lamarin ya auku ne ranar Talata da rana.

Bayanai sun ce igiyar ruwa ce ta ja matashin zuwa cikin teku a daidai lokacin da suke wanka tare da wasu abokansa su biyar.

Majiya ta ce, “Mahaifiyar yaron ta ce igiyar ruwa ce ta ja ɗanta. Sun tafi shaƙatawa ne a bakin teku tare da wasu abokansa biyar, amma shi bai dawo ba.”

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ƙara da cewa jami’ansu na yamkin sun ziyarci inda abin ya faru, kuma ‘yan uwa yaron suna zaman jiran a gano gawar marigayin.