Me ya sa maza suke ƙara aure? (2)

Daga AMINA YUSUF ALI

Assalam, barkanmu da sake haɗuwa a wani makon mai albarka. Har yanzu muna kan maganar dalilan da suke sa maza ƙara aure. Wato dalilai waɗanda ba su da alaƙa kuma da matsalolin matansu na gida. Wanda ba sai na ƙara maimaita bayanin da na yi a makon da ya gabata ba, a game da aƙidar ƙaro aure. A wannan karon, za mu dubi ɓangaren maza, kamar yadda a makon jiya muka fi mai da hankali ga mata. Amma kafin mu yi hakan, za mu cikasa sauran dalilan da suke sa maza su ƙaro aure. A wancan makon mun tsaya daga na 10. Yanzu za mu ɗora:

  1. Na sha ɗaya, cika umarnin musulunci. Wani namijin yakan ƙara aure ba don komai ba sai don cika umarnin Allah, a kan idan mutum yana da hali ya ƙaro aure iyakacin yadda Allah ya hore masa ya riƙe. Amma wasu matan za su ga kawai ba a yi musu adalci ba. Domin suna kyautata wa miji kuma ba su yi masa laifi ba. Kamar yadda na faɗa a wancan makon, kuma na nanata a wannan makon, ba laifin da kika yi. Kawai ya ƙaro aure ne saboda yana ganin ya ƙara domin yana da damar hakan.
  2. Akwai namijin zari. Shi irin wannan namijin sai an samu mace mai fahimta sosai sannan za ta iya haƙurin zama da shi. Domin namiji ne mai hange-hange da son canji kullum. Ko a harkar rayuwa kamar abinci ko motocin hawa, ko sutura ko wasu abubuwan, yana da ruwan ido. Ba ya iya amfani da abu guda na tsahon lokaci. Wannan namijin haka yake. Da zai aure dukkan matan Duniya, kuma ya hangi wata guda da ta yi saura, sai ya ji yana sha’awar ta shiga jerin matansa, ita ma ta zama tasa. Uwargida, idan kika ɗora wa kanki kishi a kan waɗanan maza kin saya wa kanki hawan jini da ciwon zuciya. Shi dai kullum ya auri wannan, ya saki waccan. Aikin kenan. Sai ranar da tsufa ya cim masa ko ranar da ba shi da arzikin auren. Kuma irin wannan za ka ga ba su fiye sakin uwar gida ba, ko wata wacce suka fahimci juna da ita a cikin matan da yake ta aurowa ba. Ko ba don komai ba, sai don ta kular masa da gida kuma da yaran da sauran matan suka bari. Domin wani daga ta yi haihuwa guda, to ta tsufa, kawai canji yake so. Wani kuma tana samun ciki, sai ya ji duk ta gundure shi. Daga ƙarshe ma wataƙila a gida za ta haihu. To irin wannan idan kina sonsa, kina son zama da shi, sai kin kau da kai a kan aure-aurensa. Kin nuna masa ke ma kina goyon baya. Idan ba za ki iya ba, ina mai ba ki shawara ki zarga wa karenki igiya kawai ki yi gaba. Maza masu wannan hali kuma su sani, don Allah ya ba ku damar ƙara aure, ba yana nufin kuma ku yi wa damar hawan-ƙawara ba. Matan nan da kake aure kana saki ƙanne da ‘ya’ya da jikokin wasu ne. Kuma duk abinda ka yi, kai ma za a yi wa zuri’arka. Haka kuma a wajen Allah akwai azaba tsattsaura ga masu auren ɗanɗano.
  3. Izza tana sa namiji ya tara matan aure. Domin ya dinga alfahari ya ce matana kaza ko yarana kaza. A qasar Hausa, an ɗauki yawan mata da ‘ya’ya a matsayin wata babbar daraja. Shi ya sa ma ake yi wa mai kuɗi ko mai sarauta kallon raini idan an gan shi da mace guda da yara kaɗan.

14.Tilastawa daga wata mace. Akwai wasu mazan da suke ƙara aure don wata mace ta tilasta su. Wato ta liƙe masa tun yana guduwa, har ta ja ra’ayinsa. Wani da tausayi, ko kyawun hali, ko kuma shi ma ya tsunduma a sonta ba tare da ya yi lissafi ba. Irin wannan kuma duk kyautatawarsa a gare shi ba lallai ta yi tasiri ba. Kuma ba don ba ya son ki ba. Kawai dai abu ne ya zo a haka. Kuma Allah ya rubuta za su yi aure. Da bai rubuta ba ma fa, ba za su yi ba. 

  1. Tausayin Uwargida: Wani namijin kan ƙara aure domin tausayin matarsa ta gida. Musamman a aikin gida ko kuma ta fuskar mu’amalar auratayya. Musamman ma idan tana da wata lalura wacce take hana ta sauke dukkan nauyin da yake kanta. 
  2. Rashin zaman lafiya na mata: Wasu mazan kan ƙara auro matar idan suna da mata biyu da suka ƙi jituwa. Hakan zai sa ya ga bari ya ƙaro wata domin su nutsu su daina zazzafan kishi da adawa da juna. Kuma ma fi yawancin lokuta idan aka ƙaro ɗin, suna zama lafiya. Musamman idan ba ka kawo ta cikinsu ba. Idan ka kawo ta cikinsu ka sake haɗa faɗa don ɗaya za ga haɗa kai da ita a sake raba maka gida. Shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Ko ya dira ta ƙafa, ko ta kai, ko ma ta zaune, dukka ruwansa. 
  3. Rashin kyautatawa/gazawar matar gida: Yanzu  mun zo kan batun dai da mata suke tsoro. Maganar gaskiya mata da yawa su ne suke yi wa kansu kishiya. Domin rashin kulawa da miji da kyautata masa tare da girmama shi. Abinda ya sa na ce mata da yawa suna yi wa kansu kishiya shi ne, domin su suke jawowa namiji ya ƙaro aure. Wani namijin ma bai da niyyar ƙarowa amma kuma matsin lamba da rashin jin daɗin aure shi zai tilasta har ya fara sha’awar ƙarin. Wasu mazan ma da gangan suke ƙaro auren a matsayin horo ko ɗaukar fansa a kan rashin biyayya da kyautatawar matarsa. 
  4. Maza suna ƙara aure don neman so: Idan aka yi wa namiji auren haɗi ko auren dole, kuma aka yi rashin sa’a matar ba ta yi masa kyautatawar da za ta shiga ransa ba, to kullum tunaninsa zai kasance yadda zai yi ya samu soyayya. To don an ji ya ƙaro aure ma, ba abin mamaki ba ne. 

Mai karatu, waɗannan dalilai na sama, suna daga cikin dalilan da suke sa maza qara aure. Wataƙila akwai wasu da yawa da ban lissafo su ba. Don haka, mata sai a hankalta a daina yamutsa hazo daga jin an ambaci kishiya. Wallahi wata kishiyar ma alkhairi ce a gare ki. Takan sa miji ya yi miki girmamawa ko alkhairin da bai taɓa yi miki ba a baya. Ko a auro wacce za ki ƙaru da ita. Allah yana tsara lamurransa yadda ya so.

Haka kuma ke ma kina so ‘yarki ko ƙanwarki ta auri mai mata ko kuma idan ke kika fito ko mijinki ya mutu, kina so wani ya aure ki. Ki dinga tunanin gaba. 

Kishiya ba yaƙi ba ce ba. Mace ba ta mutuwa don an yi mata kishiya. An yi wa matan da suka fi ki komai ma a Duniya. Kuma ba ta kashe su ko ta rage nusu daraja ba. 

Kai kuma Yayana ka sani, shi fa ƙarin auren nan ba fa sanya hula ko riga ba ne yana da sharuɗɗansa. Kuma ka san wanda ya sanya sharuɗɗan nan shi ne dai wanda ya ba ka damar ƙarin. Wato Allah (SWT). Kada garin neman gira a rasa ido kuma. Kada garin a gyara sunnah a ɓuge da kwaso zunubai. 

To ba ka da halin kula da wacce kake tare da ita ba ma, ka tafi ka jajibo wata. 

Shi ƙarin aure fa ba gasa ba ce, Yayana, kamata ya yi ka tabbatar da cewa za ka iya riƙe ta gida tare da wacce za ka ƙaro ɗin. 

Kafin ka tunkari maganar ƙaro aure, dole ka tabbatar za ka iya sauke nauyin iyalinka. Wato za ka iya ciyarwa, tufatarwa, da suturtawa da ilmantarwa, sannan da ba da haƙƙin auratayya da sauransu. Kuma ka ƙara kula da cewa, idan ka ƙara aure kuma nauyin ya ninku biyu. Ga ƙarin ‘ya’ya. Idan da a shekara 2 ana haifar yara biyu a gidanka, yanzu kuma fa bi-biyu za a dinga zubo maka. Don haka, maganin kada a yi? Kada a fara. 

Sannan ka tuna da kuɗin makaranta da yake zaune da gindinsa. A ƙara tunani. 

Sannan kuma akwai zancen yin adalci a tsakanin matanka. Allah da Kansa ya faɗa a littafinsa mai tsarki cewa, idan kana tsoron ba za ka yi adalci ba, to ka zauna da mace guda ko abinda hannunka ya mallaka. Wato kamar bayi ko kuyangi  da makamansu. 

Amma maza da yawa sun mai da ƙarin aure gasa ko wata hanyar shaƙatawa ko qasaita da isa. An yi watsi da wancan umarnin na mai dukka. Kuma duk wanda ya biye wa son zuciyarsa ya taka dokar Allah, shi ma fa ba zai ga dai-dai ba a rayuwarsa. Walau a wannan Duniyar, ko lahira. 

A nan mu ka kawo ƙarshen jawabinmu na wannan mako. Mu na godiya ga masu kiran waya da turo saƙon imel domin yi min addu’a ko godiya, ko ba da shawara, ko tsokaci. Haƙiƙa hakan yana qara ƙarfafa ni. Na gode. Sai kuma wani makon, idan Allah ya raya mu.