WASIƘU: Miladiyya 2022

*Marigayi Muhammad Awwal Musa: Mutum mai hagen nesa

Assalmu alaikum. Ba don na isa ba, magana ce mai buƙatar mu ƙara nutsuwa mu ɗauko madubi ta fuskar addini mu ga ina ne matsalar ta ke, kuma ta ina gyaran zai wanzu a sauƙaƙe. Makon jiya ne mabiya addinin Kirista su kai bukukuwan ibadunsu. Bisa zamantakewa ta makwabtaka ko wasu huldodi ana samun wasu musulmai na bazama wajen gudanar da shagulgula tare da abokan zamanmu. Duk da kasancewa ni ba malami ba ne amma ya dace idan musulmi zai gudanar da komai ya tuntuɓi malamai, shin Halal da akasinta domin kar mutum ya ɗauka cewa ai duk abinda lauje ya janyo wai ciyawa ce. Ba bu wani malami wanda ya ce a zalunci wanda ba musulmi ba. Musulumci addini ne mai koyar da gaskiya adalci da amana tare da tausayi da taimako a inda ya kamata.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa; 07066434519, 08080140820

Marigayi Muhammad Awwal Musa: Mutum mai hagen nesa

Assalamu alaikum, ’yan uwana barkanmu da warhaka. Godiya ta musamman ga mawallafin Jaridar Manhaja, Mohamed Idris, Editan jaridar, da dukan sauran ma’aikatanta.

A yau, zan yi wasiƙa ne na tunadar da juna game da abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a ta yau da kullum, inda a kullum nake yin tsokaci game da wasu abubuwan da suka shafi al’umma, musamman matasa.

A yau zan mayar da hankali ne game da bayanan rayuwa da kuma ayyuka na wani matashi, wato babban wanmu, Muhammad Awwal Musa, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 18 ga watan Agustan (16/10/1991-18/09/2019), sakamakon jinyar da ya yi fama da ita ta Sikila, wanda kimamin shekaru biyu kenan da rasuwarsa.

Muhammad ya kasance mutum ne mai kishin addanin musulunci, kuma mai son zumunci, wand aba ya son abin da ka taɓi ɗan uwansa.

Akwai halaye goma sha uku da na san Muhammad da su, waɗanda su ne;
1- Yarda da Allah
2- Adalci da rashin nuna bambamci ga kowa
3- Haƙuri
4- Taimako
5- Kasancewa mutumin kirki ga kowa
6- Tausayi
7- Tsaftar jiki
8- Aikata ayyukan ƙwarai
9- Soyayya saboda Allah
10- Yafiya ga wanda suka sava masa
11- Yawaita ayyukan lada
12- Nuna halin ƙwarai
13- Ƙaunar aikata ayyukan alheri

Muhammad ya kasance mutum ne wanda ya yi fama da wannan cuta ta Sikila tun yana da kilamin watanni shida da haihuwa, wanda kuma haka ya yi ta fama da wannan cuta, yau ciwo gobe lafiya, yau ciwo gobe lafiya, wani lokaci kuma a yi kamar ya rabu da cutar, domin ta kan jima ba ta tashi masa ba, wani tsakanin kuma ta rinƙa tashi masa akai-akai, musamman a ƙarshen rayuwarsa.

A haka wannan bawan Allah ya yi ta fama da jikin nan har ya yi karatunsa na Firame, ya yi na Sakandare, ya yi Difloma a Kaduna Polytechnic, sannan ya samu daman shiga jami’a kai tsaye zuwa jami’ar Tafawa Ɓalewa da ke Bauch, inda can ma jikin nasa ya tava tashi kamar bai zai rayu ba. A wannan kwanciya ce ma, wacce ta zo daidai suna gudanar da jaraba, a gadon asibiti Muhammadu ya yi wata jarabawar.

Bisa ganin yadda wanann jami’a ke takurawa matuƙa, mahaifinmu na ga cewa Muhamamd zai sha baƙar wahala a harkar karatu a wannan Jami’a, ya sa ya canja masa Jami’a, ko da kuwa zuwa ƙasashen wajen ne, in dai za a samu sauƙi saboda yanayin jikinsa. Inda kuwa ana cikin haka sai ya samu wani abokinsa ya samar masa gurbi a Jami’ar ISFOP da ƙasar Benin, wanda a can ya kamala karatun digiri ɗinsa.

Kamar yadda na faɗa a sama, rashin Muhammad babban rashi ne, wanda har mu ma ta mu ta zo ba za mu iya mantawa da shi ba, abu ne da a kullum sai mun tuna shi. Wannan ne ya sa na yi fama da mahaifanmu, ina ta lallashinsu musamman ma mahaifiyarmu, wacce ta jima kullum sai dai mu ji ta tana faman sheƙa kuka.

Duk wanda ya san Muhammad kuma ya yi hulɗa da shi zai ga cewa ya yi mu’amala da mutanen kirki, wanda ya san dattako, mutumin da ke girmama duk wanda ya ci karo da shi.

Muhammad ya kasance tamkar aboki ne a wurina, duk da na kasance ƙaninsa, wanda duk inda za mu je muna tare da shi, duk wata shawara tare muke yenta.

Ina faɗin waɗannan abubuwa da halaye na wannan mutum ne a kaina, wanda ba ni kaɗai ba, haka yake wajen mahaifansa. Shi ke tuƙa su zuwa yawancin wuraren da suke son zuwa, shi ke ake aike kusan duk harkokin gidan, shi ne wanda suke ambata da ‘babban Sakatare.’

Akwai abubuwa da dama, waɗanda in ina tuna su game da Muhammad hankalina ya kan tashi, musamman a kwanakinsa na ƙarshe a duniya, a lokacin da ya kwanta a asibiti. Idan jikin ya ɗan lafa masa mukan yi hira, wasu abubuwan da muke tattaunawa da shi ba za su faɗu a nan ba, domin abuuwa ne da ke sa mutum kuka da zurfafa tunani.

Lokacin da aka zo yi wa Muhammadu jana’iza na ga tururuwar jama’ar da ban taɓa tunanin ganinsu ba, na ji bayanai game da shi daga abokai da maƙwabta waɗanda ban taɓa sanin Muhamamd ya kai wannan matsayi ba a rayuwarsa, ballanta abubuwan da ’yan uwansa na uwa da uba ke faɗi game a shi.

Akwai abubuwan faɗa da dama game da Muhammad, amma ba abin da za mu ce illa Allah ya gafarta masa, ya sa kyawawan ayyukansa su bi shi, ya kankare masa zunubansa, ya sa aljanna ce makomarsa. Mu kuma Allah ba mu haƙurin jure wannan rashi, ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe. Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968